✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mad Air ya shirya wasan Polo don hada kan ’yan Arewa

Kyaftin kuma shugaban tim ddn wasan kwallon Polo na Mad Air da ke Katsina Alhaji Lawal Mangal ya ce ya shirya wasan polo ne don…

Kyaftin kuma shugaban tim ddn wasan kwallon Polo na Mad Air da ke Katsina Alhaji Lawal Mangal ya ce ya shirya wasan polo ne don kara hada kan ‘yan wasa musamman na Arewa.  Wasan Polo an shirya shi ne na kwana uku da aka kare a ranar Lahadin da ta gabata a filin wasan polon da ke gonar da aka fi sani da Gonar Dikko Ladan da ke kan hanyar Jibiya.
 Kamar yadda jagoran ya ce ,Mad Air ya gayyato zaratan ’yan wasan da suka hada da Hamisu Buba da Madani Sani da Alwan Umar da Suwidi Abdalla da Farouk Adam Gumel da sauransu tare da Dawakai kusan 40.
“Mun hada wannan wasa ne don kara dankon zumunci da kuma neman  zama tsintsiya madaurinki daya musamman wadanda suka fito daga yankin Arewa.. Sanin kowa ne harkokin wasa na daya daga cikin abubuwan dake hada kan al’umma, shi ya sa muka zabi wannan lokaci na Azumi don neman albarka.”
 Alhaji Lawal ya nuna damuwarsa akan irin yadda aka samu rabuwar kawuna a tsakanin Hukumomin da ke shirya wasan Polo watau NPF da kuma NPA wanda ya ce dukkansu suna da manufa daya a kokarin ciyar da wasan polo gaba.
Idan za a tuna a bara ma kamfanin Mad Air ya gabatar da irin wannan wasa na sada zumunta a daidai wannan lokaci.