Godiya ta tabbata ga Allah wanda Yake da cikakkiyar siffa, wacce ba ta da tawaya ko kadan kuma har abada, Ya bayyana falalarsa ga mata da maza, kuma Ya shari’anta wa mace da ta gyara kanta da hijabi domin ta zama abin koyi wajen ladabi da kyawun hali, kuma don ta kange mazaje game da kallon tsiraicinta, ta yanda hakan zai sa kowanne ya wayi gari cikin kyawun hali. Tsira da amincin Allah su tabbata a bisa ga ManzonSa, wanda ya ce ku zauna da mata da kyakkyawar kulawa. Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kare kanku (Da iyalinku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu…”
Duk wanda ya yi riko da wasiyyar Manzo (SAW) wajen yin mu’amala da mace kamar yadda ake yin mu’amala da zinari ko azurfa, tsararriya wacce ba don komai ake tsare da su ba face don kyawunsu da tsadarsu. Kuma kar ku yi mu’amala da ita kamar yadda kuke mu’amala da abu mai arha wanda ake samu kodayaushe, wanda kuma kowa na iya samunsa duk lokacin da yake bukata, kuma kar mu so ta zama kamar ‘yar wuta, domin Manzon Allah (SAW) yana cewa (Akwai wasu mutane! Har yanzu ban gansu ba, daga cikinsu sai ya ambaci wasu mata wadanda in ka gan su za ka ga da kaya a jikinsu amma dai tsirara suke, karkatattu ne game da yi wa Allah biyayya, kuma masu karkatar da wasunsu ne game da bin hanyar Allah, kawunansu kai ka ce tozon rakumi ne wanda ya ke a karkace, Manzon Allah ya ce ba za su shiga Aljanna ba, kuma ma ba za su ji kamshin Aljannar ba).
Ya ke ‘yar uwata Musulma! Lallai abin da ake nufi da mace mai bayyana tsiraici ita ce wacce take sanya tufafi matsattsu, ko mai shara-shara, ko budadde, ko gajere, ko kuma wacce take barin gashinta a bude kowa na gani da makamancin hakan.
Amma dai wacce take mumina ta gaske, tsarkakarkiya, wacce take son tsarkin zuciya da kuma kamun kai, wacce ba ta yarda da abin da na ambata a baya ba sakamakonta shi ne aljanna kamar yadda Annabi (SAW) ya ce: “Idan mace ta yi salloli biyar, kuma ta yi azumin watan Ramadan, ta kiyaye farjinta, ma’ana ta kange al’auranta game da bayyana tsiraici da fitinuwar mutane da ita, kuma ta yi wa mijinta biyayya, za a ce da ita: ki shiga aljanna ta kowace aofar da kike so.
A karshe ya ke ‘yar uwa mai karamci! Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Ka sanar da bayina, lallai ni mai Yafewa ne kuma Mai jinkai, kuma lallai azabata ita ce azaba mai radadi”.
Idan kina son hanyar yafiyar Ubangiji, to ki riki sharuddan hijabi wacce shari’ar Musulunci ta yarda da su kamar haka:
1. Ya zamanto hijabin ya rufe jiki baki daya 2. Kar hijabin ya zama ado a karan kanshi 3. Ya zamo mai duhu ne ba mai shara-shara ba 4. Ya zama yalwatacce ba matsattse ba 5. Kada ya yi kama da kayan maza 6. Kuma kada ya yi kama da kayan kafirai 7. Kada kuma ki sa turare in za ki fita, domin Manzon rahama yana cewa duk macen da ta shafa turare sannan ta fita ta wuce wasu mutane domin su ji kamshin da take dauke da shi na turare to ita mazinaciya ce 8. Kuma kada ki yi domin ya zama ado. Ya ‘yar uwa furen musulunci!
Me ke rudar ki ne? Shin ba ki san Allah yana ganinki ba? Ki farka domin muna da bukatar shiryuwarki, muna rokon Allah Ya kiyaye mu da ‘yan uwan maza baki daya.