✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aurata 53 ake zargin sun hallaka abokan zamansu a shekara biyu

Akalla ma’aurata 53 ne aka kiyasta sun aika abokan zamansu na aure zuwa lahira, a nan Najeriya tun daga ranar 19 ga watan Nuwamban 2017,…

Akalla ma’aurata 53 ne aka kiyasta sun aika abokan zamansu na aure zuwa lahira, a nan Najeriya tun daga ranar 19 ga watan Nuwamban 2017, ranar da Maryam Sanda ta kashe mijinta, zuwa yanzu kamar yadda binciken Aminiya ya nunar.

Watanni 26 bayan kashe mijin nata da ta yi, a farkon makon nan kotu ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A ranar 24 ga Nuwamban 2017, ‘yan sanda suka gurfanar da ita gaban kuliya kan mutuwar mijin nata, Bilyaminu Bello, wanda da ne a wajen tsohon Shugaban Jam’iyar PDP, Alhaji Bello Halliru Muhammad.

Da yake karanta hukuncin a ranar Litinin din makon nan, alkalin kotun Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya bayyana cewa hujjar da Maryam din ta gabatar wai mijin nata ya mutu sakamakon faduwa da ya yi kan tukunyar shan tabar shisha, soki burutsu ne kawai.

Ya bayyana cewa, karkashin ka’idar ganin karshe, wacce aka yanke wa hukuncin lallai ne a kanta ta bayyana sular mutuwar mamacin, ba wai bangaren masu shigar da karar ba, sakamakon ta yadda cewa ita ce ta yi masa ganin karshe.

Koda yake batun na sanda da Bilyaminu, yam utu guda ne kawai cikin batutuwa makamantan wannan inda ma’aurata ke rasa rayukansu a hannun abokan zaman nasu da ke kara ta’azzara cikin shekarun baya-bayan nan.

Wani mai suna, Bamidele Olanrewaju dan shekara 40, ya fada komar rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, bisa zargin ya lakadawa matarsa Adenike, dukan kawo wuka wanda hakan ya yi sanadin rasa ranta.

Kamar yadda kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi, ya fada a Abeokuta lamarin ya faru ne ranar Lahadi 19 ga watan Janairun 2020 a kauyen Bisodun yankin Ofada a Karamar Hukumar Obafemi-Owode, inda ma’auratan ke zama.

An yi zargin mutumin ya yi amfani da wani katon sanda inda ya yi ta jibgarta har sai da ta sume. Bai tsaya nan ba, sai da ya yi amfani da sukul direba  inda ya daba mata shi a ka, har sai da ta ce ga garinku nan.

A wani bangaren mai kama da wannan, wani dan shekara 60 a garin Île-Ife, cikin Jihar Osun mai suna Rafiu Irawo, ya kashe matarsa Funke, inda shi ma ya kashe kansa bisa zargin wai matar tana cin amanar aurensu da wani farkarta.

Lamarin ya wakana ne a unguwar Alakowe cikin garin Ile-Ife, ranar Juma’a 20 ga watan Satumban bara.

Har wa yau, an zargi wani mai suna Akorede Balogun da laifin cewa ita ce ta hallaka mijinta, Rasaki Balogun, wanda aka tarar ya mutu tare da farkarsa Misis Muyibat Alabi, a cikin gidansa mai lamba 16, kan layin Taiwo Oke, a rukunin gidajen Victory Estate, da ke Ejigbo a birnin Lagos ranar 10 ga Yulin 2019. Ganau, Oguegbu Promise, ya fada wa ‘yan jarida cewa, Misis Balogun din ta yi amfani da karfi wajen dura wani ruwa da ake zargin wata guba ce a bakin mamacin.

Wani matashi dan shekara 37 mai suna Mutiu Sonola, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun sakamakon dukan matarsa, mai suna Zainab Shotayo, har rai ya yi halinsa.

Cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun Kakakin Rundunar a jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne ranar Laraba 25 ga watan Disamba 2019, bayan mahaifin matar ya gabatar da kokensa gaban ofishin ‘yan sandan Ibara.

Lamarin baya-bayan nan, mai kama da wadannan, shi ne a ranar 27 ga watan jiya, daidai karfe  4 na alfijir, inda can ma wata mai shekara 19, mai suna Rabi Shamsuddeen, an yi zargin ta daba wa mijinta, Shamsuddeen Salisu, dan shekara 25, wuka a ciki. Ya faru ne a kauyen Danjanku cikin Karamar Hukumar Malumfashi Jihar Katsina.

Bayanai sun ce, lamarin ya faru ne sakamakon rashin fahimtar juna tsakanin ma’auratan. Makwabta sun ce bayan sun ji kururuwar neman dauki daga mamacin, ba tare da bata lokaci ba suka yi wa wurin tsinke inda suka tarar yana rarrafe domin fita daga kuryar dakin jini nata zuba daga raunin da aka yi masa a ciki, sa’annan suka garzaya da shi asibiti. An kuma ce makwabtan sun shaida ganin matar tsaye kusa da wajen tana rike da wuka dauke da jini ya mamaye ta.

Wasu cikinsu ma an ruwaito sune suka garzaya da mamacin zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Akwai rahotannin faruwar lamari irin wannan a dukkan fadin kasar. Binciken Aminiya, ya gano cewa wasu mata 36 ne aka bayar da rahoton mazansu suka kashe su, yayin da maza 17 kuma aka bayar da rahoton matansu suka hallaka su.