Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanya sayen Romelu Lukaku daga Inter Millan a kan Fam miliyan 97.5.
A ranar Alhamis Lukaku, dan wasan gaban kasar Belgium ya sanya hannu a takardar kwantaragin kan Yuro miliyan €115. Shi kuma zai rika samun Yuro miliyan 12 bayan haraji a karshen kowace kakar wasanni, baya ga kudaden tallace-tallace.
Bayan rattaba hannun, Chealsea ta ruwaito Lukaku yana cewa: “Ina farin cikin sake dawowa wanna kulob mai matukar ban sha’awa. Na goyi bayan Chelsea a lokacin da nake dan karam.
“Yadda kungiyar ke tafiya ya yi daidai da burine kuma bayan lashe gasar Serie A. Wannan damar ta zo a daidai, kuma za mu sanu babbar nasara a tare.”
Lukaku ya bar Chelsea ne a Gasar cin Kofin UEFA na 2013, a wasan da ya barar da bugun fenariti a karawarsu da Bayern Munich.