✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littattafan ’yan darika ke kafirta su ba ’yan Izala ba – Sheikh Ahmadu Maidankoko

Sheikh Ahmadu Maidankoko sanannen malami ne musamman a Kudancin kasar nan. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce littattafan ’yan darikar Tijjaniyya ne suke kafirta su…

 Sheikh Ahmadu MaidankokoSheikh Ahmadu Maidankoko sanannen malami ne musamman a Kudancin kasar nan. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce littattafan ’yan darikar Tijjaniyya ne suke kafirta su ba ’yan Izala ba, inda ya yi kira ga ’yan darikar su koma ga sahihiyar akida ta Musulunci kamar yadda aka saukar wa Annabi (SAW):

Aminiya:  Allah gafarta Malam ka ce kana da jan hankali ga al’ummar Musumia kan mene ne?
Sheikh Mai dankoko: Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu alan nabiyyil karim. To abin da nake so na ja hankalin Musulmi a halin yanzu shi ne, a gaskiya Musulmi sun saki hanya, ba sa yin addinin nan kamar yadda aka saukar da shi. Ya kamata su kama sahihiyar hanya ta koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) kamar yadda aka saukar masa kuma ya bar mana.
Aminiya: Ka gano ana yin wani abu ne da ba daidai ba ya sa kake cewa a koma kan daidai?
Sheikh Mai dankoko: Eh, a zahirin gaskiya ya kamata Musulmi na gaskiya su bar bin wasu hanyoyi na wasu shaihunnai na darika, alhali kuma su shaihunnan nan ba wahayi aka yi musu ba. Babu wanda ake yi wa wahayi sai Annabi kuma Annabi Muhammadu (SAW) shi ne karshen Annabawa kuma a karshen rayuwarsa aya ta sauka cewa addinin nan ya kammala, ba wani da Allah zai sake aikowa da sako.
Wadannan shaihunnai ba su zo da komai ba, kawai so suke su daukaka kansu su azzama kansu, suna fada wa jahilan mutane cewa su ne wani abu, idan an bi su za a yi kudi, kuma idan an bi su za a samu gafara ko idan ka gan su Allah Ya gafarta maka, idan an gan su za a shiga Aljanna. Wallahil azimu karya suke yi.
Aminiya:  Shaihunnan darika da kake nufi na da ne ko na yanzu?
Sheikh Mai dankoko: Shaihunnan darika da na da da na yanzu duk aikinsu ke nan, idan ba haka ba ina hujjar da mutum zai ce Annabi ya dawo duniya bayan ya shekara dubu daya da dari daya da hamsin da barin duniya? A ce Shehu Tijjani ya ce ya ga Manzon Allah (SAW), ya zauna sun yi hira da Manzon Allah (SAW), har Manzon Allah (SAW) ya ce masa Salatul Fatihi kafa daya ta fi saukar Alkur’ani sau dubu shida.
Wai kuma a zahiri ba a mafarki ba, ga shi ga Annabi (SAW), yana yi wa Manzon Allah (SAW) tambayoyi, Manzon Allah (SAW) yana ba shi amsa. Duk wani shaihi ko na ina ne a nan duniya, ko na Najeriya ko na Kaulaha na kalubalance shi ya kawo hujja idan ba a rubuta haka ba a cikin littattafansu ba. Wannan haka yake a rubuce a cikin littafinsu mai suna Jawahirul Ma’ani. Idan Manzon Allah (SAW) zai dawo duniya ya fadi wata magana babu wanda zai fadawa sai sahibinsa Abubakar Siddiku da Umar da Usman da Aliyu (RA).
Idan aka duba cikin littafinsu na Jawahirul Ma’ani shafi na 137, mai Salatul Fatihi cewa ya yi saukar masa da ita aka yi, bayan ya shiga cikin Ka’aba ya shafe shekara 40 yana ibada a ciki, yana rokon Allah Ya ba shi salatin da ta fi kowace, ta fi Alkur’ani, ta fi duk abin da Manzon Allah (SAW) ya fada a duniya. Sannan ya ce sai Mala’ika ya zo masa da ita Salatul Fatihi a cikin takardar haske. Ka ga wahayi ke nan kuma ba a yi wa wani mutum wahayi bayan Manzon Allah (SAW). Kuma mene ne matsayin mutumin da ya ce ya roki Allah Ya ba shi abin da ya fi Alkur’ani ya fi abin da Manzon Allah ya zo da shi ko ya fada?  
Aminiya: Malam kana nufin ba a kan daidai suke ba ke nan duk tsawon shekarun nan har da wadanda suka rasu?
Sheikh Mai dankoko: Wallahi wadanda suka riga mu gidan gaskiya ina rokon Allah Ya gafarta musu, domin Allah bai sa sun yi bincike sun gane ba ko kuma ba su ga wadannan littattafai ba. Duk wanda ya yi bincike a cikin Alkur’ani ba zai taba yarda cewa ga wani mutum ya shiga Ka’aba ya zauna kwana arba’in wanda Annabi Ibrahim bai yi ba, haka dansa Annabi Isma’ila da suka gina Ka’aba tare bai yi haka ba.  Haka Annabi Muhammad (SAW) bai taba shiga Ka’aba ya kwana 20 ba, ko goma ko bakwai. Sannan wani mutum da ba Annabi ba, ba Manzo ba, ya yi haka kuma a yarda? Sannan an ce duk wanda ya karanta wannan salati sau daya tak an ba shi ladan saukar Alkur’ani fiye da sau dubu shida, wato an kaskanta Alkur’ani ke nan. Idan sun ce wannan sufanci ne, an taba jin Sayyadina Abubakar ko Abu Huraira ya ce ga wani abu idan an karanta shi ya fi a sauke Alkur’ani sau dubu shida? A nuna mana a ina takardar hasken take. Na kalubalanci duk wani malami a Najeriya. Billahillazi la Ilaha illa huwa idan ya kawo takardar hasken nan na ba shi gidana.
Aminiya:  To idan ka ce haka, daga ina darika ta samo asali?
Sheikh Mai dankoko: Wannan akidar ba daga Musulunci take ba, ta Yahudawa ce. Yahudawa su dama bukatarsu kurum su rushe addinin Allah. A cikin sahabban Annabi (SAW) da tabi’ina da tabi’it tabi’ina babu wanda ya taba fadar irin wannan kalma cewa Annabi (SAW) ya fada masa. Annabi ya ce duk wanda ya aikata wani aiki da babu umarninsa ko na Allah to wannan aikin ba karbabbe ba ne a wurin Allah. Ina kira ga shaihunnan darikar Tijjaniyya da mukaddamansu da muridansu su tuba ga Allah su daina yin abin da suke yi, sun bar koyarwar Manzon Allah.
Kuma akwai wasu maganganu biyu da Shehu Tijjani ya yi da nake so a fada kowa ya ji. A cikin littafinsa Yakutatul Faridah, ya ce zai shigar da mabiyansa cikin Aljanna ba tare da an yi musu hisabi ko azaba ba. Kuma ya ce ko ka yi zunubin duk duniyar nan zai shigar da kai Aljanna. Manzon Allah (SAW) ya taba fadar haka?  
Aminiya:  Ba ka jin ko yana da wata fassara ta daban?
Sheikh Mai dankoko: Babu wata fassara wacce za mu yarda da ita da ta shige wacce take cikin Alkur’ani. Na biyu kuma Shehu Tijjani ya ce shi Annabi ne, ya fada ya ce shi yana cikin Annabawa har ma yana da matsayi na Annabi arba’in. Idan ko wani zai ce ko almajirinsa ne ya rubuta, to, me ya sa da ya gani bai yi magana ba? Don haka irin wadannan abubuwa da ke cikin littattafansu ne ke kafirta duk wanda ya yarda da su, ba ’yan Izala ke kafirta su ba. Su fito su ce wadannan abubuwa kuskure ne sun barranta daga gare su mana. Martanin da na yi wa Sheikh dahiru Bauchi a kwanakin baya kuwa a cikn jarida har yanzu ya kasa ba ni amsa. Ka je ka duba jaridar ka gani mana. Kuma a kan irin wannan bayanin na yi masa.