✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Litinin za a yi jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai Zagaye na biyu

A ranar Litinin 11 ga watan da muke ciki ne za a yi Jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) zagaye na biyu. Jadawalin…

A ranar Litinin 11 ga watan da muke ciki ne za a yi Jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) zagaye na biyu.

Jadawalin zai gudana ne a Hedkwatar Hukumar  UEFA da ke Nyom a kasar Suwizilan.  Za a kasafta kungiyoyi 16 ne da suka haye zuwa mataki na biyu na gasar.  kungiyoyin da suka zama na farko a yayin gudanar da wasannin zagayen farko na gasar za su hadu da takwarorinsu da suka kasance na biyu ne.  Kenan kowace kungiya za ta iya haduwa da wacce ta kasance ta biyu.  Alal misali kulob din Manchester United zai iya haduwa da kulob din PSG ko Jubentus ko Real Madrid ko Chelsea.  Kamar yadda FC Barcelona za ta iya haduwa da Real Madrid ko PSG ko Jubentus ko Chelsea.

Kamar yadda jadawalin da hukumar UEFA ta fitar ya nuna a ranar 13 da 14 da kuma 20 da 21 ga watan Fabrairun 2018 ne za a fara yin wasannin farko, yayin da a ranakun 6 da 7 da kuma 13 da 14 ga watan Maris ne ake sa ran za a yi wasanni karo na biyu.  Daga nan ne za a sake zubar da kungiyoyi takwas yayin da takwas kuma za su haye matakin kwata-fainal.

kungiyoyin da suka hayewa zagaye na biyu na Gasar Zakarun Kulob Na Turai:

1. Manchester United

2. Basel

3. PSG

4. Bayern Munich

5. Roma

6. Chelsea

7. FC Barcelona

8. Jubentus

9. Manchester City

10. Shaktar Donestk

11. Besiktas

12.  Tottenham

13. Real Madrid

14.  Sebilla

15.  Liberpool

16.  FC Porto