A ranar Litinin mai zuwa ne kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles za ta fara wasanta na farko da Iran a cigaba da wasannin cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil.
Wasan zai gudana ne da misalin karfe takwas na dare. Sannan a ranar ce kuma ake sa ran kasar Fotugal za ta kece raini da Jamus da misalin karfe biyar na yamma yayin da Ghana kuma za ta hadu da Amurka da misalin karfe sha daya na dare.
Najeriya tana bukatar ta samu nasara a wasan ne don ta samu karfin gwiwar tabuka abin a-zo-a-gani a gasar amma idan ta kuskura Iran ta doke ta a wasan farkon to akwai matsala.
Sauran kungiyoyin da za su fafata a gasar sun hada da Bosniya Herzgobina da kuma Ajantina.
A ranar Asabar 21 ga watan Yuni kuma ake sa ran Najeriya za ta yi wasanta na biyu da kasar Bosniya Herzegobina da misalin karfe 11 na dare.
… Yadda Mikel Obi da Emenike suka kusa yin dambe a Brazil
Rahotanni da ke fitowa daga Brazil sun nuna an samu sabani a tsakanin biyu daga cikin ’yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles watau John Mikel Obi da kuma Emenike.
Wadannan fada da ’yan kwallon suka yi ta sa aka samu rarabuwar kawuna a tsakanin ’yan kwallon da ke goyon bayan Mikel da kuma wadanda ke goya wa Emenike baya.
An ce dambarwa a tsakanin ’yan kwallon biyu ta samo asalin ne jim kadan bayan Najeriya ta yi canjaras da kasar Girka a wasan sada zumunta sannan abin ya sake tsananta jim kadan bayan da Amurka ta doke Najeriya da ci 2-1 a wani wasan sada zumunta a makon jiya.
’Yan kwallon sun rika caccakar juna ta fadin bakaken maganganu al’amarin da ta sa Koci Stephen Keshi ya shiga tsakani kuma ya hore su da su tuna Miliyoyin ’yan Najeriya a gida sun zuba ido ne su ga yadda za su fafata a gasar cin kofin duniya don fitar da kasar kunya amma abin bakin ciki sai ga shi suna neman bata rawarsu da tsalle.
Daga baya dai kocin ya sasanta su kuma ya ba su umarnin su nemi gafarar juna inda nan take suka amince kuma suka sha alwashin hakan ba za ta sake faruwa ba.
A ranar Litinin mai zuwa ne dai ake sa ran Najeriya za ta fara wasanta na farko da kasar Iran.
A wasanni uku na sada zumunci da Najeriya ta yi da kasashen Sukotlan da Girka da kuma Amurka, Najeriya ta yi kunnen doki ne a wasanni biyu, yayin da ta samu rashin nasara a wasanta da Amurka.