✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitan bogin ya kashe mutum 15 wajen  tiyata a Adamawa

Jami’an tsaron farin kaya na DSS da ke Yola a Jihar Adamawa sun kama wani da ake zargin likitan bogi e mai Ibrahim Mustapha bisa…

Jami’an tsaron farin kaya na DSS da ke Yola a Jihar Adamawa sun kama wani da ake zargin likitan bogi e mai Ibrahim Mustapha bisa zarginsa da laifin yi wa majinyata 15 tiyata kuma duka suka mutu.

Likitan wanda yake dauke da shaidar karatu ta Hukumar Ilimin Kimiyya da Kere-Kere (NBTE), yana aiki da Gwamnatin Jihar Adamawa ne a matsayin likita duk da ba ya da takardar shaida zama likita kimanin shekara biyar da suka wuce.

Aminiya ta samu labarin cewa a tsakanin shekara 5 ne Ibrahim Mustapha ya rika yi wa majinyata tiyata inda hakan ya sa 15 daga ciki suka mutu.

Rahoto ya ce Ibrahim ya yi aiki a asibitoci da dama a kananan hukumomin Mayo-Belwa da  Fufure.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar,  DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kama Ibrahim Suleiman.

Wani jami’in tsaro da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun rundunar ’yan sanda inda ake ci gaba da  tuhumarsa.

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a lokacin da Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Adamawa ta kai masa ziyara a shekaranjiya Laraba, ya bayyana kaduwarsa game da labarin da ya samu na likitan bogin.  Ya ce tuni ya kafa kwamitin da zai binciko yadda al’amarin ya faru kuma duk wanda ke da hannu wajen ba likitan aiki alhalin bai mallaki shaidar zama likita ba, zai fuskanci hukunci.