✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Leken Asirin Wayar Maigida (3)

Shawarwarin Masu Karatu Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za…

Shawarwarin Masu Karatu

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga karin bayanan da kuka aiko a kan matsalar leken asirin wayar maigida; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1. Na amfana matuka da dukkan bayananki na farko da na biyu dangane da matsalar leken asirin wayar miji. Ina son ku kara jan hankalin ‘yan’uwa mata sosai, domin wannan babbar matsala ta haifar da mace-macen aure da dama har ma da ni din nan, haka ta faru da ni. Matata tana yawan tambayata wai nawa ne albashina a wata, ni kuma naki fada mata don sirrina ne, ba lallai sai ta sani ba. To ranar da aka yi mana alert na shigowar albashi, bayan mun yi barci, dare ya raba tsaka, na bar wayar tana caji; sai ta farka ta dauki wayar da sunan za ta haska ta je kewaye alhali kuma tana da tata wayar, ta shiga ta ga dukkan sirrina da na boye a cikin wayar. Na farka don in duba wayar ko lokacin Sallah ya yi, sai na ga ba waya ita kuma ba ta dakin. Sai na nufi kewaye na ganta a zaune tana ta dubawa da binciken wayar wanda ni kuma raina ya yi matukar baci na bata takardar sakin aure take a nan.
Mafi yawan mata su kan duba sirrin wayar maigida ne ba domin zarginsa da neman mata ba sai don kasancewa yanzu waya ta zama rumbun tanadarwa da ajiye dukkan sirrin dan Adam, kama daga albashinsa da dukkan mu’amular shigowa da fitowar kudi, da dukkan bayanan dukiyarsa da ke banki da ma adadin albashin da yake karba tare da dukan kololuwar sirrinsa da baya so matansa ko ‘yan’uwansa su sani; tare da sauran muhimman bayanan sirri da ya adana a wayarsa wanda bai kamata mace ta bincika masa ba.
Kuma don Allah ku yi jan kunne ga matan da suke binciken akwatunan maigidansu, wadurof, mota ko aljihun maigida don dai ganin sirrinsa.
-Muhammad Katsina.
2. Da mata, har da mazan za su aikata shawarwarin da aka bayar a wannan fili da sun hutar da zuciyoyinsu da sake-sake. Bai dace ma’aurata su rika aikata irin wadannan aiyuka ga junansu ba; domin irin wannan binciken ba ya haifar da komai face bacin rai. Shi ya sa Allah (SWT) ya ce “Kada ku yi leken asirin juna!” Shi aure ana gina shi ne a kan yarda, kauna da tausayin juna; su ne ginshikin zaman aure, idan aka rasa daya za a samu matsala.
3. To ai su ma mazan ya kamata ku ja masu kunne su bar barin irin wadannan kazaman abubuwa cikin wayoyinsu. Ni maigida baiyi mini iyaka da wayoyinsa ba, hatta yaranmu ba ya hana su daukar masa waya su duba ,wani lokaci ma shi yake kunna masu games ya ba su suna yi. A irin haka ne kawai rannan na sami danmu dan shekara takwas ya budo wani bidiyo na batsa yana kallo a cikin wayar Babansa. Hankalina ya kara tashi bayan na bincika wayar sosai na ga hotunan matan banza tsirara na tabbata ba ranar yaron ya fara budo irin wadannan kallace-kallace ba. Saboda haka su mazan ma ku ja masu kunne, duk wani abu da in an gani zai haifar da fitina tsakaninsu da matansu, da kuma abubuwan fitsara bai kamata su rika bari a cikin wayoyinsu ba. In har ya zama dole su yi hulda da ‘yan mata, ya kamata duk namijin da ya san ciwon kansa da ciwon iyalansa ya rika kokarin boye duk wasu munanan abubuwa daga ganinsu. Kullum magidanci ya rika tsabtace wayarsa yana goge duk abubuwan da ganinsu ga matarsa ko wani daban na iya zubar masa da mutuncinsa. Mu kuma mata mu ji tsoron Allah, mu daina son bin diddigin sirrin mazajenmu, kuma har in mun gano wani sirri mu bar shi tsakaninmu da Allah mu bar yada shi ga kawaye da ‘yan’uwanmu.
– Maman Aliyyu daga Kebbi
4. A gaskiya duk matar da ta san abin da take yi ba za ta binciki wayar maigidanta ba domin za ta gano wa kanta tashin hankali domin Allah ya sani duk matar da take binciken wayar mijinta to wallahi tana tare da bacin rai, domin a gaskiya dole da namiji ya yi hulda da mata ko yana so ko ba ya so; wani ma’aikaci ne, wani dan kasuwa ne; balle uwa uba kuma dan siyasa. Saboda haka don Allah ‘yan’uwa mata mu san abin da muke yi, zaman aure fa ba zaman barkatai ba ne, zama ne na ibada; yadda za ki yi Sallah Allah ya ba ki lada, to haka idan kika farantawa maigidanki rai Allah ba zai barki haka ba.
-Hajiya Binta Alkali Kano.
Da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.