✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA

Wata makwabciyata ce mai juna biyu ta wuce lokacin haihuwarta, da ta je asibiti aka ce za su rike ta su sa mata magungunan haihuwa,…

Wata makwabciyata ce mai juna biyu ta wuce lokacin haihuwarta, da ta je asibiti aka ce za su rike ta su sa mata magungunan haihuwa, sai ta gudo, tana cewa ita nakudarta ba ta zo ba, tunda ba ta jin ciwon nakuda. To mece ce illar gudowar da ta yi?

Daga Makwabciya Ta Kirki

 

Amsa: E, tabbas akwai matan da lokacin haihuwarsu zai zo amma mahaifa ta yi biris ta ki fara nakuda, har sai an sa mata ruwan magani. A likitance wannan sai ya wuce sati 40 wato watanni 10, ko a ce idan ta wuce lokacinta da sati biyu (lokacin da aka rubuta a katinta). Idan likitoci sun auna sun kuma gani a katinta da kuma hoton scanning cewa lokacin haihuwarta ya wuce, gata suka yi mata idan sun ce ta kwanta a sa mata maganin haihuwa, domin wuce lokacin haihuwa babbar illarsa ita ce ta rasa jariri, wato zai iya mutuwa a ciki. Kin ga kuwa ba karamar asara ba ce a dau juna biyu watanni 10 a zo a rasa shi. Don haka ki ci gaba da ba ta baki har sai ta yarda ta koma. Ko ki sanar da maigidanki ya sanarwa maigidanta illar hakan don kada a zo abu ya baci a ce a matsayinku na makwabta ba ku yi abin da ya dace ba.

 

Me ke kawo kumburin kafafu da kuma ciwo a mata alhali ba wani juna-biyu ba ne da ita?

Daga Khadeeja Zarewa.

 

Amsa: Ai ko a mai juna biyun ma kumburin kafa mai radadi da ciwo ba lafiya ba ne, ballantana a wadda ba ta da juna biyu.  Akwai abubuwa da dama da za su iya kawo hakan tun daga kiba, zuwa ciwon sanyin kashi, zuwa ciwon hanta zuwa ciwon koda, zuwa na zuciya duk za su iya kawo hakan. Don haka duk mai samun irin wadannan alamu sai an duba an tantance dalili.

 

Mene ne muhimmancin shan zuma ga yara?

Daga Sulaiman kiru, Kano

 

Amsa: Kowa zai iya shan zuma, babba da yaro. Duk muhimmancin daya ne kamar a manya wato cewa ita zuma banda sugan fructose tana da sinadarai masu yakar cutuka a jiki, abin da muke cewa inflammation da kimiyyance. Sai dai kawai a lura wasu yara za su iya samun borin jini kamar kuraje ko zawo idan sun sha zuma, wato jikinsu bai karbe ta ba. To idan aka ga haka kada a takura sai an ba su.