✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin zaki da bera

Barka da warhaka Manyan Gobe fatan alheri gare ku, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin zaki da bera. Labarin…

Barka da warhaka Manyan Gobe

fatan alheri gare ku, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin zaki da bera. Labarin na kunshe da darussa da dama, yana kira a taimaka wa dan uwa don ba a san abin da gobe za ta haifar ba.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin zaki da bera

Akwai wani zaki a wani daji da ake kira ‘dam’. Bayan zaki ya ci ya koshi sai barci mai nauyi ya dauke shi a karkashin wata bishiya. Can sai ga bera ya zo ya fara wasa a kansa. Zaki ya ji kamar ana wasa a kansa, sai ya farka don  ya ga abin da ya tayar da shi daga barci. Daga baya ne ya yi ido hudu da bera.
bera sai ya razana. Zaki ya ce sai ya kashe shi, sai bera ya ba shi hakuri. Kamar zaki zai kashe shi, can sai ya hakura ya bar shi.
Rannan bera ya zo wucewa sai ya ga zaki cikin shingen maharbi, sai bera ya je ya yanke shingen maharbi da hakoransa ya bar zaki ya fita. Tun daga nan sai suka zama abokai.
To, Manyan Gobe, da  a ce zaki bai hakura a lokacin da bera ya ba shi hakuri ba, da bai samu wanda zai cece shi lokacin da ya fada shingen maharbi ba. Da fatan Manyan Gobe za su zama masu taimako da hakuri a duk inda suka tsinci kansu a ciki.