✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Tunkiya da Karen daji

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da karen…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da karen daji. Labarin ya kunshi yadda tunkiya ta ki bin shawarar da karen daji ya ba ta.
A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi

Labarin Tunkiya da Karen daji

Wani masifaffen karen daji ne ya yi yawon neman abinci bai samu ba. Idanunsa duk sun yi jajawur sakamakon yunwar da ta addabe shi, duk da haka bai hakura ba ya ci gaba da yawo, ana cikin haka sai ya hango tunkiya daga nesa, sai ya sanya a ransa cewa ya samu abinci.
Daga nan sai ya fara tafiya a hankali don kada tunkiya ta gano shi ta gudu.  Ana cikin hakan, sai ta gano manufar karen daji, sai ta ruga a guje ta shiga wajen bautar gumaka ta buya. Karen daji ya yi iya kokarinsa domin ya kamo tunkiya amma ya gagara.
Rashin kama tunkiya sai ya sa ransa ya baci, daga nan ya sassauta murya, ya kira tunkiya, ya ce mata ta fito waje domin idan har boka ya kama ta zai yi layya da ita.
Tunkiya ta yi murmushi ta ce da shi, ai gara a yi layya da ita maimakon ya cinye ta. Jin hakan sai ya gane cewa ba ta da niyyar fita. Sai ya yi fushi ya tafi.
To, Manyan Gobe, da tunkiya ta bi shawarar karen daji kuna tsammanin za ta tsira? Don haka, kada ana rika daukar shawarar makiya.