Wasu malaman Islamiyya sun yi nadamar yada labarin karya cewa wata yarinya mai shekara 11 ta rataye kanta saboda an hana ta kallon talabijin.
Malaman sun nuna nadamar tasu ce a wani zama da magabata suka yi da su domin sanin inda suka samu labarin da suka yada a shafukansu na sada zumunta ba tare da sun binciki gaskiyar lamarin ba.
Malaman sun nemi iyayen yarinyar su yafe musu, suna masu cewa sun yi aiki ne da jita-jita, ba tare da bincike ba suka yi wa’azi a kai, aka kuma yada a kafafen sada zumunta.
Da yake yi wa Aminiya bayani, mahaifin yarinyar, Dakta Muhammad Aminu Bello Sarkin Jamfalan, wanda malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya nuna damuwarsa kan yadda malamai suka yada irin wannan labarin ba tare da sun bincika ba.
Ya ce an yi ta yadawa cewa ’yar tasa ta rataye kanta ne saboda an hana ta kallon wani shirin gidan talabijin na Arewa 24 alhali ba gaskiya ba ne.
Ainihin abin da ya faru
Dakta Muhammad Aminu Bello ya ce, “A tsarin gidana yara ba su damu da kallon talabijin ba.
“Kusan tun kan a haifi yarinyar, tsawon shekara 12, talabijin daya ne a gidan, kuma a dakin hutawana.
“Don haka yarinyar ta dawo daga makaranta ne sai ta dauki abincinta ta shiga dakin ’yan uwanta don ta ci.
“To bayan kamar minti biyar da shiganta, da kaninta ya ga bai gan ta ba sai ya bi ta, da yake ya yi ajiya a dakin, don kar ta taba mishi, sai ya bi ta.
“Yana shiga sai ya same ta a kwance a kasa, sai ya dauka ko tana mishi wasa ne, ya taba ta, ya ji ba ta motsi, sai ya kira yayansu.
“Shi ma da ya zo ya ga haka sai suka kira mamansu, tana zuwa sai ta mirgina ta, sai ta ga alama ba ta motsawa kuma a kanta ga rauni.
“Sai suka kira wata ma’aikaciyar asibiti da muke makwabta da su ta duba ta tabbatar da mutuwarta.
“To a ranar, bayan kammala jana’iza muna karbar gaisuwa da jama’a sai ga labari a kafafen sada zumunta cewa wai ’yata rataye kanta ta yi.
“Wai wani malami ne ya yi wa mata wa’azi cewa budurwa ta rataye kanta a kan an hana ta kallon shirin Arewa24, kamar yadda ka sami labari, alhali ba haka ba ne.
“Don haka muka nemi su wadanda suka yada labarin don mu ji ina suka sami wannan labari.
“A matsayina na malamin makaranta ina ba al’umma shawara da su daina biye wa duk irin wadannan kafafen da suke yada shiri kuma lallai ne gwamnati ta dauki matakin gyara a irin wadannan kafafe na sada zumunta.”
A ranar Litinin din makon nan ne wasu malaman makaranta suka watsa labari ta kafafen sada zumunta cewa wata yarinya mai shekara 11 a Zariya ta rataye kanta saboda an hana ta kallon wanin shirin talabijin.