✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Raliya a gidan aure (2)

A makon da ya wuce, mun fara kawo muku labarin wata baiwar Allah, wadda rashin iya girki ya haifar mata da matsala a rayuwar aure.…

A makon da ya wuce, mun fara kawo muku labarin wata baiwar Allah, wadda rashin iya girki ya haifar mata da matsala a rayuwar aure. Mun kai daidai lokacin da ta fara bayar da labarinta, inda ta nuna su uku aka haifa a gidansu na attajirai, kuma ita kadai ce ’ya mace. Ga cigaba:
“Na samu gata, wadda duk wanda ya same ta, zai yarda shi dan gata ne. Mahaifana ba sa son bacin raina. Wanki, wanke-wanke, girki da duk wani aiki ban iya ba.
“Mahaifanmu sun tanadar mana ’yan aiki. Babu abin da na fi kwarewa da shi a duniya kamar barci, sai ko kallon fim da kuma yawace-yawace. A lokacin, kawayena suna sha’awar rayuwata. Hakan ya sanya na taso ban iya komai ba, ban kuma mayar da hankali na koya ba.” Ta sake yin shiru, wanda hakan ya sa na kara tattara hankalina gare ta.
Ta ci gaba: “Wata rana muna hira da mijina Auwal (ba sunansa na gaskiya ba) kafin mu yi aure, sai ya ce mini babu abin da yake buri face matarsa ta yi masa girki mai dandano, domin bai yarda wata ko wani ya rika dafa masa abinci ba; ba zai kuma lamunce wa cin abinci a gidajen sayar da abinci ba. A lokacin ban dauki zancensa da mahimmanci ba, sai ban yi wani yunkurin koyon girki ba.
“A ganina, yadda yake so da kaunata idan na marairaice masa zai tausaya mini mu dauki masu girki. Ashe abin ba haka yake ba.”
Muryarta ta yi rauni, na ji ta koma kasa-kasa, mai dauke da birbishin kuka. Na gyara zama domin a karo na farko na ji zuciyata ta raunana, domin ina da yakinin an zo gabar da ta fi sosa mata rai. Bayan ta yi ta ’yan maza ne, sai ta ci gaba:
“Mun fara samun matsala da shi ne mako biyu bayan aurenmu. A ranar, bayan mun sha shayi, ya kuma kimtsa zai fita, sai ya ce na dafa masa tuwon shinkafa da miyar taushe kafin ya dawo. Bayan na marairaice masa don kada ya fita ne, a karshe na yi masa rakiya har bakin kofar gida. Bayan ya fita ne, sai hankalina ya tashi.
“Domin yau ce rana ta farko da ya ce na dafa masa abinci. Ban yi kasa a gwiwa ba, sai na kira kawata a kan ta zo ta taya ni girki, sai ta ce mini bari ta tambayi izinin mijinta. Daga baya ta kira ni ta sanar da ni mijinta bai ba ta izini ba. Na kara rikicewa.  Haka na rika kiran kawayena, amma ban samu wacce za ta taya ni ba, kowace da irin uzurinta.
“Dole ta sa na kira mahaifiyata na sanar da ita halin da ake ciki. Sai ta turo mini daya daga cikin masu aiki a gidanmu. Bayan ta zo muka shiga kiciniyar girki, sai dai tun kafin mu gama sai Auwal ya dawo.” Ta sake yin shiru.