Assalamu Alaikum. A yau na kawo muku wani labari ne mai jan hankali, firgici da motsa zuciya ga duk wani uba da ke son ya sauke nauyin da Allah Ya dora masa na tarbiyar ‘ya’yansa.
Labari ne na Nura, wanda ya kasance mai kirki kuma yana son jama’a, sannan kuma gashi mai son karatu da haddar kur’ani mai girma. Amma sai dai kash!
Nura ya taso iyayensa na son shi matuka, musamman mahaifiyarsa wadda take masa kallon dan lele. Shi ma mahaifinsa na sonsa sosai. Ita mahaifiyarsa tana sonsa ne irin so da kauna irin na uwa da da. Shi kuma mahaifin na sonsa ne saboda shi ne babban dansa na miji. A tunaninsa, shi ne zai yi karatun BOKO, ya zama wani babban mutum da zai magance masa TALAUCI a lokacin da ya tsufa ya yi ritaya daga aiki.
Nura ya taso yana son karatu sosai kuma yana yin karatun. Tun yana karami mahaifin ke fafutukar neman ya yi karatu mai inganci. Kullum mahaifin yana kai-kawo ne a kan ya tabbatar da cewa Nura ya samu karatu mai inganci. Don haka ne ya sanya Nura a makarantar kudi har ya kammala karatun Firamare.
Bayan ya kammala Firamare, sai mahaifin ya dauki Nura ya tura shi Sakandirin kwana, duk da cewa mahaifiyar Nura ta nuna rashin amincewarta, kuma abokanan mahaifin sun nuna masa cewa ya kamata ya lura da cewa yawancin makarantun kwana ba sa lura da tarbiyar addini. Amma shi da yake tunaninsa kawai yadda Nura zai samu ingantaccen ilimin boko ne, sai ya yi burus, ya dauki Nura zuwa makarantar kwana.
Yana zuwa ziyara makarantar akai-akai domin ganin halin da dansa ke ciki. Kullum idan ya je makarantar, sai malaman Nura su kawo masa takardu da suke nuni a kan cewa Nura na kokarin karatu. Hakan ke sanya wa ya yi farin ciki da murna. Amma sai dai kash! Bai taba tambayar Nura ko ya masa fada a kan tarbiya ko karatun addini ko su waye abokanansa ba.
Daga baya Nura sai ya hadu da wani aboki mai suna Musa Alaramma. Shi dai Musa dan malamai, kuma yana da tarbiya mai kyau. Haduwar Nura da Musa ke da wuya, sai Nura ya fara sha’awar zama mahaddacin Alkur’ani mai girma.
Ana cikin haka sai watarana mahaifin Nura ya zo makarantar da niyyar ya ga Nura. Koda ya zo makarantar, sai malaman suka shaida masa cewa kwana biyu Nura ya canja daga yadda suka san shi a baya. Kullum yana Masallaci yana karatun Alkur’ani, ya rage karatun boko. Hankalin mahaifin sai ya tashi. Ya je masallaci ya samu Nura yana karatu, amma maimakon ya yi murna, sai ya daure fuska. Hankalin Nura ya tashi, sai ya ce “baba me ya sa ka daura fuska maimako ka yi murna. Ni na fi son Alkur’ani fa a kan karatun bokon nan, kuma ko takardun da ake nuna maka, in fada maka gaskiya ba nawa bane. Suna nuna maka ne kawai saboda kana musu kyauta. Amma har ga Allah ba na gane karatun bokon nan sosai. Don haka ina so ka karfafa mani gwiwa in zama mahaddacin Alkur’ani.”
Mahaifin Nura sai koma gida yana ta fada, yana zage-zage, wai ai ba karatun kur’ani ya kai shi ya koya ba. Mahaifyar Nura ta tambaye shi me ke faruwa, sai ya shaida mata halin da ake ciki. Ita kuma sai ta fara dariya da murna tana cewa danta ba shaye-shaye da rashin tarbiya ya fara ba. Sannan ta nuna wa mahaifin day a dauki kaddara ya goya wa Nura baya, amma ya ce shi atafau ba ruwansa da Nura.
Tun lokacin da mahaifin Nura ya gano cewa ba zai samu abin da yake a wajen Nura ba, sai ya tsani Nura, ba ya ganin komai na alheri daga gare shi, kullum nemansa da sharri kawai yake yi. Hasalima said a yak ore shi daga gidansa. Ya ce ya koma gidansu Musa.
Ana cikin haka har Nura ya kammala karatun Sakandare, amma bai samu wani ilimi ba wanda ya wuce rubutu da karatu, amma a bangaren kur’ani, ana iya cewa ya zama gangaran. Har ya samu nasarar zama gwarzon shekara a wajen karatun kur’ani. Amma duk da hakan, mahaifin nasa na jin haushi, wai saboda bai tsaya ya yi karatun boko ba. Amma ita mahaifiyarsa kullum tana cikin murna da jin dadi. Shi kuma kullum mahaifin cewa yake yi wai laifin mahaifiyar ne.
Nura ya shiga cikin damuwa da tunani na yadda mahaifinsa ke jin haushinsa. Watarana yake fada wa malaminsa cewa, “Mahaifina sai a hankali, bai taba tambaya ta ya ibada ba. Kuma haka yake ko a gida. Ban taba jin ya tambaya kannanaina da yayyina karatun addini ko ibada ba. Idan zan zauna a gida in wuni ban fita na je masallaci ba, ba zai taba min fada ba. Ban taba jin ya je makarantar Islamiiyar da muke zuwa ba domin ganin yadda muke karatu, amma kullum yana ziryar zuwa boko ya tambaya ya karatunmu. Haka akwai wani kanina, shi kuma bai son karatun boko, amma yana kokari wajen sana’ar hannu, amma shi ma bai sonsa. Shi dai kawai duniya ya sa a gaba, amma abin takaicin shi ne, shi bai ma san haka yake ba. Shi a tunaninsa ya san abin da yake yi. Idan ka masa magana sai ya ce maka ya fi ka sanin abin da yake yi, idan har ma ka samu ya saurare ka ke nan. Don Allah baba ka karfafa min gwiwa in zama mahaddacin kur’ani domin ba zan iya boko ba. Allah ba zai tambayeka ilimin boko ba, tambayar da za a maka shi ne idan ka kiyaye ni da sauran iyalanka daga shiga wuta.”
Za a iya samun Isiyaku Muhammed a lambar waya kamar haka: 07036223691