✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Malam Halilu da dansa

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata  kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Malam Halilu da…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata  kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Malam Halilu da dansa. Labarin na kunshe da darasin bai kamata a rika tsananta wa Manyan Gobe ba.
A sha karatu lafiya.
Taku:  Amina Abdullahi

Labarin Malam Halilu da dansa

Malam Halilu mutum ne mai kwazo da hazaka, amma mahaifinsa mutum ne mai kwiya, har ma aka saka masa suna ‘kasasshe’. Wannan abu ba karamin bata wa Halilu rai yake ba. Domin gudun kada wannan sunan ya biyo shi, sai ya shiga dako. A hankali ya tara kudinsa ya sayi fili, inda ya mayar da wurin gida da kuma gona.
Ginin gidan nasa na tabo ne, kuma yana da mata hudu. Babban dansa na da shekara 12. Gudun kada wannan mummunan sunan ya biyo shi da iyalinsa ya sa ya shiga noma. Shi da babban dansa da matarsa suna fara aikin gonar ne daga zarar an yi sallar asuba. Kuma ba za su huta ba sai an kira sallar Magriba.
Matansa da dansa abin na ba su haushi, amma babu wanda zai iya fitowa fili ya bayyana korafinsa sakamakon wahalar da suke sha a aikin gonar. Domin suna bukatar hutu.
Idan ana aikin sai babban dansa ya je bayan gida ya dade. Da abin ya yi yawa sai Halilu ya gano cewa dansa na kwiya ne. Sai ya fara masa fada yana dukansa. Ya ce masa ba ya son da rago.  Sakamakon yanayin yadda babban dansa ya girma. A kullum aka gan shi sai a rika ganinsa fuska a daure. Har aka aza cewa ba ya fara’a. Daga nan ya rika rashin lafiya, saboda wahalar da kya yake sha. Da kyar aka ceto rayuwarsa. Mahaifinsa ya fahimci illar hakan, daga nan ya rika sassautawa.
To iyaye sai a kula. Za a iya sanya yara aiki amma ba wanda ya fi karfinsu ba.

Sanarwa
Manyan Gobe za ku iya turo da hotunanku zuwa wadannan adireshin imel: [email protected] ko [email protected]
Ku rika sanya cikakken sunanku kafin ku turo da hotunan.