Jarumin nan a masana’antar fina-finan Kudancin Najeriya ta Nollywood, Jim Iyke, ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya karbi addinin Musulunci.
A ranar Laraba ce dai labarin cewa ya shiga addinin na Musulunci ya fara yawo a shafukan sada zumunta, inda aka rawaito cewa ya shiga ne ta hannun Babban Limamin Jihar Imo.
- Badakalar biliyan N80: EFCC ta sako dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris
- ‘Amfani da man bilicin na iya haifar da ciwon koda’
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, jarumin ya ce asalin hotunan da ake yadawa daga cikin wani fim aka dauka da suka yi a kasar Ghana.
Ya ce, “Ina ganin ya kamata na yi karin hasek kan wani labari da ya karade gari. A mafi yawan lokuta, ban cika yin tsokaci a kan jita-jita ba, saboda ba su shafe ni ba. Amma akwai layin da bai kamata a tsallaka ba.
“An dauko hotunan ne daga wani fim da muka yi a kasar Ghana kan tsattsauran ra’ayin addini, amma suka kare a hannun wani mai neman yada jita-jita. Ko da yake ba ni da matsala da Musulunci, amma ba ni da wata niyya ta shiga addinin ko a yanu ko kuma a nan gaba,” inni Jim Iyke.