✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Ali da barayi 40

Barka da warhaka Manyan Gobe Assalamu alaikum,  Manyan Gobe da fatan kuna lafiya. Allah Ya sa haka. Na kawo muku labarin Ali da barayi 40.…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Assalamu alaikum,  Manyan Gobe da fatan kuna lafiya. Allah Ya sa haka. Na kawo muku labarin Ali da barayi 40. Labarin zai koya wa Manyan Gobe yadda yin kirki ke taimaka wa mutum.
A sha karatu lafiya.
Labarin Ali da barayi 40

An yi wani makeri  da ake kiransa Ali. Yana da kwazon aiki da kuma taimaka wa iyalinsa daidai gwargwado. Rannan ya tafi daji farauta, sai ya ci karo da barayi 40 a kan dawakansu. Da ganin dawakan, sai ya tsorata ya hau wata bishiya ya buya. Sai ya ga abin mamaki. Babban barawo ya sauko daga dokinsa ya je kusa da wani dutse mai suna ‘sasame’. Bayan ya je ne sai ya ce “ ka bude ya kai sesame!”, can sai dutse ya bude. Babban barawo ya shiga cikin dutsen. Bayan dakiku kadan sai ya fito suka koma inda suka fito.
Abin ya ba Ali mamaki sosai, sai ya sauko daga kan bishiyar ya je gaban dutsen ya ce “ka bude ya kai sesame”, sai dutsen ya bude. Ali ya ga abin al’ajabi bayan ya leka cikin dutsen, babu komai a ciki sai gwalagwalai. Sai ya debi kadan ya wuce gida ba tare da sanin cewa wasu gwalagwalan sun zube a hanya ba.
Bayan kwana biyu da barayi suka dawo sai suka ga alamar cewa an shiga dutsen. Sai babban barawo ya ce a nemi wanda ya yi sabon arziki a gari. Da aka bincika, sai aka ga Ali ne.
Ali kuma ya riga ya bunkasa, domin ya bude shago kuma yana da baiwar da ke taimaka masa. Ya dauki baiwar tamkar ‘yarsa, yana kuma kyautata mata.
Rannan da daddare sai ta ga wani barawo ya je da alli ya yi shaida a gidan Ali. Ita kuma sai ta yi irin shaidar a gidajen makwabtan Ali. barayi sun yi kokarin kashe shi amma abin ya gagara.
A karshe dai baiwar ta kama barawon wata rana da ya shigo gidan Ali da takobi. Amma ta tona asirinsa, hakan ya sanya  Ali ya aura mata dansa.
Ali mai kirki ne kuma ba ya bambanta masu aikinsa da ‘ya’yansa. Da a ce ba ya kyautata wa jama’a da barayi sun dade da kashe Ali.