✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labari da dumiduminsa: Daya ga watan Satumba ne ranar babbar sallah—Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar ya ayyana 1 ga watan Satumba na shekarar 2017 a matsayin ranar babbar…

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar ya ayyana 1 ga watan Satumba na shekarar 2017 a matsayin ranar babbar sallah.
Hakan yana kunshe ne a sanarwar da Shugaban Kwamitin Shawarwari Kan Al’amuran Addinin Musulunci na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu ya sanya wa hannu.
Sanarwar wacce Kamfanin Dillancin Labari na Najeriya ya samu kwafinta a garin Sakkwato a ranar Laraba ta nuna cewa ayyana ranar ta biyo bayan ganin jinjirin watan Zulhijja da ka yi a ranar Talatarda ta gabata.
“Kwamitin shawarwari da hadin gwiwar kwamitin kasa kan ganin wata sun sami rahoton ganin wata a sassa da dama na kasar nan inda suka tabbatar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talatar da ta gabata ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2017”. Inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sakamakon haka ne Musulmin Najeriya za su yi idin babbar salla a ranar daya ga watan Satumba.
Sanarwar ta bayyana cewa Sarkin Musulmin ya taya Musulmi murna tare da fatan samun shiriyar Ubangiji.