A jibi Lahadi ake sa ran za a yi wasa mafi zafi a wannan mako a gasar La-Liga ta Spain karo na 14. Wasan zai gudana ne a tsakanin kulob din Atletico Madrid da na FC Barcelona da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya.
Kawo yanzu Barcelona ce take matsayi na farko da maki 28 a wasanni 13 sai Real Madrid ta biyu da maki 28 sai Sebilla a matsayi na uku da maki 27 sai Atletico Madrid a matsayi na hudu da maki 25.
Ke nan duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta, za a ba ta tazara ganin yadda kungiyoyin suke bin juna da maki 1 zuwa uku a tsakani.