✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyautar injin taliya ba aikin dan majalisa ba ne – Barista Hassan

Wani lauya mai zaman kansa dan fafutukar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma Barista Garba Hassan ya bayyana cewa ba da kyautar injin taliya da…

Wani lauya mai zaman kansa dan fafutukar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma Barista Garba Hassan ya bayyana cewa ba da kyautar injin taliya da wasu daga cikin ‘yan majalisa ke yi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.

Garba Hassan ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 ya yi bayani karara game da ayyukan ‘yan majalisa saboda haka aikin dan majalisa yin dokoki ne ba raba injin taliya ba.
Barista Hassan ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Talata da yamma.
Daga lokaci zuwa lokaci zan rika zantawa da manema labarai domin wayar da kan talakawan kasar nan game da hakkokinsu da ke kan shugabannin da suka zaba.
A cewarsa, da yawa daga cikin ‘yan majalisun Kudancin kasar nan suna ba da kulawa ta musamman wajen gabatar da korafe-korafen mutanen yankinsu a zauren majalisa, amma ’yan majalisar Arewa sun fi ba da fifiko wajen raba injin taliya wa talakawa.
Daga bisani ya yi amfani da wannan dama, inda ya bayyana cewa, yana kira da babbar murya ga talakawa da mu guji siyasar gina ciki, domin ba za ta haifar musu da da mai ido ba.