✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kyautar Allah: ’Yar sanda ta haifi ’yan uku

’Yan ukun da ’yar sandan ta haifa sun hada da maza biyu da mace daya.

Wata ’yar sanda ta haifi ’yan uku, maza biyu da mace daya a ranar Laraba.

Mai jegon da ta haifi ’yan ukun na daga cikin ’yar sandan masu tsaron matar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Edward Ajogu.

  1. Yadda Fani-Kayode ya hada ni da Nnamdi Kanu — Asari Dokubo
  2. Mun gano Ministar da ta sayi kadarar Dala miliyan 37 a boye — EFCC

Kwamishinan ’Yan Sandan tare da wasu jami’ansa sun ziyarci mai jegon domin yi musu barka da karuwar da aka samu.

Ajogun ya ziyarce su ne a yankin Kemta da ke birnin Abeokuta inda ya nuna jin dadinsa tare da yi wa Allah godiya kan karuwar da abokiyar aikin tasu ta samu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya yi wa mai jegon kyautar kudi.

Shi ma shugaban PCRC a jihar, Arch. Samson Kunle Popoola, ya yiwa ’yar sandar da ta haihu kyautar kudi.