✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyandir ya yi ajalin ’yar shekara daya a Kalaba

Ina amsa kiran sai aka ce na zo fa dakina gobara ta kama

Wutar kyandir ta yi ajalin wata yarinya ’yar shekara daya da haihuwa a duniya mai suna Kate Dickson a Jihar Kalaba.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Etta Agbor da ke Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba.

Tsautsayin ya wakana ne yayin da mahaifiyar yarinyar mai suna Glory Erin Akpan ta kunna kyandir din a daki kuma ta fita sayen magani a wani kantin sayar da magunguna da ke makwabtaka da su.

Wakilinmu da ya zanta da Glory Etim ta shaida masa cewa, diyarta na fama da larurar mura da tari.

“Sai na shimfideta na kunna mata kyandir na dora shi a kan wani karfe da na saba ajiye shi idan na kunna.

“Sai na tafi kantin sayar da magunguna domin saye mata maganin mura da tari bayan na fita da kamar minti talatin haka sai naji kira a wayata ta hannu.

“Ina amsa kiran sai aka ce na zo fa dakina gobara ta kama,” in ji ta.

Mahaifiyar yarinyar ta ci gaba da cewa, cikin hawaye na baro kantin sayen maganin a sikwane na zo gida na samu dakina cin wuta.

“Makwabta kuma sun yi bakin kokarinsu domin ceto yarinyar amma kaddara ta riga fata.

“Ko da na bude dakin sai na ga wuta ta riga ta cinye yarinyar har ta mutu.”

Wadansu makwabta da suka bukaci a sakaya sunansu, sun shaida wa wakilinmu cewa ba su da masaniyar lokacin da matar ta fita kasancewar kowa na dakinsa kuma babu wanda ta sanar a cikinsu.