✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam sun kama motar jami’a makare da tabar wiwi

Jami’an Kwastam sun daƙile ƙoƙarin wasu ɓata gari na yunƙurin fasa ƙwaurin tabar wiwi a cikin motar safa mallakin Jami’ar Noma Ta Gwamnatin Tarayya (FUNAAB)…

Jami’an Kwastam sun daƙile ƙoƙarin wasu ɓata gari na yunƙurin fasa ƙwaurin tabar wiwi a cikin motar safa mallakin Jami’ar Noma Ta Gwamnatin Tarayya (FUNAAB) da ke Abekuta.

Da yake wa manema labarai ƙarin haske, Kwaturolar rundunar a Jihar Ogun, Sani Madugu ya bayyana cewa hukumar ta kama motar jami’ar ne maƙare da tabar wiwi irin wadda ake matse ta a leda a maida ita tamkar littafi. Ya ce an samu irin wannan ƙunshi har guda 211, waɗanda aka binne su a ƙarƙashin buhunan shinkafar da aka yo fasa ƙwaurinta, sannan aka so a badda kama ta hanyar amfani da motar jami’a.

Ya shaida wa Aminiya cewa binciken da suka yi ya nuna cewa babu sanya hannun shugaban jami’ar ko wasu manyan ma’aikatanta a cikin badaƙalar.” Direban motar ne da wasu ɓata gari ke da hannu dumu-dumu, kana za mu miƙa shi tare da tabar wiwin ga hukumar hana sha da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi domin su zurfafa bin cike.”

Hakazalika rundunar ta yi nasarar kama buhun shikafar da aka yo fasa ƙwaurinta har guda dubu 2 a cikin kwanaki 10 kacal da motocin alfarma da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 40.

Da yake ƙarɓar tabar wiwin da direban motar jami’ar da aka kama, babban jami’in rundunar hana sha da fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi a Jihar Ogun, Malam Bala Fagge ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar ta yi nasarar kawar da noman tabar wiwi a faɗin jihar sai dai babban ƙalubalensu shi ne, yadda wasu ɓata gari ke yin noman ta a kan iyakokin ƙasar Benin, inda akan yo fasa ƙwaurinta, a ci kasuwarta a ƙasar nan. Ya ce tabar wiwi na da matuƙar illa ga matasa, waɗanɗa su ne kashi 90 bisa 100 na mutanen da ke ta’ammali da ita. “Kasancewar matasa su ne ƙashin bayan kowace ƙasa, gurɓatar tarbiyyarsu abu ne mai matuƙar haɗari. Don haka alhakin ya rataya a kan wuyan kowa da ya yi ƙoƙarin ba da gudunmawarsa domin kare ƙasarmu,” inji shi.

Bincike ya nuna cewa ƙasar nan kan zamo wata kasuwa wacce masu fasa ƙwaurin tabar wiwi daga ƙasashen Ghana da Kwatano kan baje kolinsu na mugunyar sana’ar da kan ba su ƙazamar riba.