✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam a Oyo sun kama buhunan shinkafa fiye da dubu daya

Kwanturola Elisha Dabid Chikan, na Hukumar Kwastam a jihohin Oyo da Osun ya ce ta kama kaya da suka hada da buhunan shinkafa sama da…

Kwanturola Elisha Dabid Chikan, na Hukumar Kwastam a jihohin Oyo da Osun ya ce ta kama kaya da suka hada da buhunan shinkafa sama da dubu daya da kananan motoci da tsofaffin tayoyin mota da suturun gwanjo masu darajar kudi fiye da Naira miliyan 55.

Ya ce jami’ansa sun yi nasarar kama kayan ne a cikin makonni uku, a sassa daban-daban na jihar ta Oyo. Mafi yawancin kayan an kama su ne a kan hanyar Oyo zuwa Ibadan a yayin da aka yi fasa kwaurin shigowa da motocin ta cikin dazukan da ke garin Saki, a kauyen Aleniboro da ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Benin.

Ya ce direbobin manyan motocin da ke dauke da buhunan shinkafar da aka kama sun yi  kokarin yaudarar jami’an Kwastam cewa suna dauke da buhunan siminti ne a cikin motocin amma binciken kwakwaf ya sa asirinsu ya tonu. Su kuma kananan motocin suna yin badda kama ne da suke dora doya a saman buhunan shinkafar.

Ya ce wannan nasara da rundunar Kwastam ta jihohin Oyo da Osun ta samu, ya biyo bayan irin taimakon da babbar hedkwatarsu a Abuja da FOU shiyyar A da ke Ikeja a Legas suke bayarwa ne. Haka kuma ya jinjina wa wasu mutane musamman mazauna kan iyakokin kasa da suke taimaka masu da labarai a boye, a game da masu fasa kwauri a yankin.

Ya kara da cewa an kama mutum 3 da ake zargin suna da hannu wajen ayyukan fasakwaurin, wadanda za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.