Editan Aminiya, wadda ta samu karbuwa a wannan kasarbaki daya, ka ba ni dama in bayyana takaicina kan yadda Gwamna Kwankwaso ya sanya mu tagumi, a tsawon mulkinsa, tun daga 1999 zuwa 2003, dakuma dawowarsa a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2014. Hakika rusau din da aka yi a titin Ibrahim Taiwo, an cutar da mu, domin gidajen tun a shekarar 1934, Gwamnatin Arewa ta bai wa Alhaji Alhassan dantata, kuma mahaifinmu ya sayi wasu a hannun dan uwansa, Alhaji Sanusi dantata, cikin shekarar 1964. Sannan ’yan KAROTA ma ba mu dadinsu ba, domin kai da kanka ka bayyana cewa ba masu ilimi ka sanya ba. Sannan Mai girma Gwamna muna zargin ka rushe masallatai a kalla 401. Akwai al’amura da dama wadanda idan muka bayyana su sai a ce adawa ce kawai, amma hakikanin gaskiyarmu muke bayani a kai. Don haka akwai bukatar ka wanke kanka kafin wa’adin mulkinka ya kare, ko kuma, wadanda aka zalunta su ci gaba neman hakkinsu wajen Allah. Daga Sabo Muhammad Ilori, Gida Mai Lamba 64, Unguwar Gabari.
Sakonnin waya
Buhariyya-Akida
Muna mika sakon bangajiya ga dimbin jama‘ar da suka halarci taron kungiyar magoya bayan Janar Muhammadu Buhari mai suna ‘ Buhariyya-Akida‘. Wadda aka gudanar a wannan Litinin da ta gabata, a garin Hadejia da ke Jihar jigawa. Da fatan kowa ya isa gidansa lafiya. Allah ya taimaki janar Baba Buhari, ya ba shi mulkin Nijeriya.
Daga: Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.
Ga shugabannin Arewa
Salam Edita barka da aiki ina so ka ba ni dama inyi kira ga shugabanin Arewa cewa ya kamata su tashi tsaye gurin ceto al’ummar yankin daga wanan hali da muke ciki a yan zu na rashin tsaro da ci gaba na yau da kullum da fatan za su tausaya mana don ci gaban yankin namu dama kasar baki daya. Daga Umar Idirisa Bapps Askira jihar Borno 07034478412.
Martani ga Muktar Shagari
Maganar da ya yi na cewa, shugaba Goodluck ya yi ayukan alheri a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce, “Goodluck ya yi aikin Titi a Gusau zuwa Kontagora,” wannan magana zukitamalle ce, don gaskiya kowa ya san cewa titin Sakwato da na Shagari da na Tambuwal da na Aleiro da na Jega da na Koko da na Yawuri da na Kontagora duk sun zama tarkon Mutuwa. Don haka Muktari Shagari da ma munsan dacewa ‘ba’a mugun sarki, sai mugun Bafade. Komai nisan jifa kasa za. Allah ya raka taki gona.
Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. Gsm 07037697009.
Addu’ar tsari daga zalunci
Edita ka ba ni dama don in isar da addu’ar neman tsari ga al’ummar Najeriya. Don haka ma nike ganinmu karanta Suratul Munafikun kafa 10, don Allah ya kawo mana karshen zalunci da makircin munafukan kasar nan. Daga A.A. U 08151767785.
A kula da direbobi
Aminiya don Allah ina da fatawa, Wai me yasa gwamnati ba ta kulawa da direbobi ne? Misali hanyarmu ta Kaduna zuwa Legas ba kula da ita, kuma me yasa haka? Daga Ibrahim 08054517672.
Ga Sarkin Kano
Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka ba ni dama in mika sakon taya murnar Babbar sallah gaMaimartaba Sarkin Kano. Da fatan ya yi sallah lafiya, tare da iyalansa. Allah Ya kara wa Sarki lafiya da nisan kwana. Amin. Daga Yunusa Hamza 08133183507.
Ga’yan takarar APC
Edita kabana dama in roki ya takarar shugabancin kasar nan a APC ,wadanda suka hada da Kwankwaso da Atiku da su hakura su bar wa Buhari takara. Domin mu dai a fadin Arewacin Najeriya ba mu da kamar Janar Muhammadu Buhari Mai gaskiya. Muna kuma rokon Gwamna Kwankwaso da ya tsayar mana da Janar Jafaru Isa amatsayin dan takarar Gwamnan, domin shi ma yana da nagartar da ta fita sauran ’yan takara a jihar Kano. Muna fatan Allah Ya yi mana zabi mai amfani. Ya kuma ba mu basira kada mu yi zaben tumun dare. Daga Ahmad Tiga 08068643445.
Ga Aminiya
Salamu alaikum. Aminiya da fatan kun yi sallah lafiya. Allah Ya maimaita mana. Kuma ya jimamin makaman da ake shigowa da su don wargaza Najeriya. To, Allah Ya tsare mu daga sharrin masu makirci. Amin. Daga 08126466663.
Ga jama’ar Arewa
Salam. Jama’ar Arewa Musulmi da Kirista mu hada kai,mu manta da bambanicin kabila da na addini. Don mu gudu tare, mu tsiratare. Allah Ya kara tona asirin masu shirin wargaza mu. Amin. Daga 08059044449.
Ga Janar Buhari
Aminioya ’yar aman don Allah ku mika min sakon “Barka da Sallah” ga jagoran APC na kasa, Shugaban asa na 2015, Janar Muhammadu Buhari, tare da al’ummar Musulmin duniya baki daya. Da fatan an yi sallah lafiya. Daga Musa Unguwar Mai Yasin, danja, Jihar Katsina 08155648155.
Mu dage da addu’a
Ya ku ’yan uwana talakawa,ba zargin shugabanni ne mafita ba. Hakan ma kara kawo mana bala’I yake yi.. Mu dage da addu’a. Daga 08079156747.
Ga Sarakunan gargajiya
Sarakunan gargajiya, na ga kun yi hawan sallah, amma waccan sallar da tagabata,wato aramar sallah, ba ku yi hawa ba. Kun ce saboda matsalar tsaro. To yanzu tsaron ya ingant ane. Ku fadi gaskiyar abin da ya hana ku hawa. Daga 08117896000.
Barkada sallah
Edi Mubarakun ga daukacin Musulmin duniya.Kuma muna addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Nagode Edita. Daga 07060799679.
Ga dan sanda mai lambar yabo
Editan Aminiya ina taya dan sanda kula da ababen hawa”Traffic Police,”da shugaban kasa ya karrama da lambar yabo. Daga 08034275846.
Ina Ibrahim Kwastom?
Edita Allah Ya kare mana kai. Ina son ka yi mana cigiyar abokina Ibrahim Custom, wanda ke zaune a Sabon gari Zariya. Domin kwana biyu bamu ji duriyarsa a Aminiya ba. Ko ya daina rubutu ne? Daga 08167569141.
Ga Gwamna Wamako
Edita ka bani dama in mika sakona ga Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako, Sarkin Yamma kan alkawarin da ya yi mana na hanya da gada a Dukamaje. Daga Alhaji Sani Abubakar Dogon Daji 08032238844.
Ga Takai dan takarar Gwmnan Kano
Fatan alheri ga dan takarar Gwamnan Kano a karkashin tutar jam’iyyar PDP, Malam Salihu Sagir Takai. Da fatan ya yi sallah lafiya. Allah Ya yi jagora. Daga 08166835313.