Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP na daya daga cikin manyan ’yan takarar Shugaban kasa a zaben gobe Asabar saboda nagartarsa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano sau biyu yana takara ce a karkashin karamar jam’iyya da ba san ta ba sosai, to amma saboda mamayar da ya yi a Kano, jihar da ta fi kowace yawan wadanda suka yi rajistar zabe da kuma dimbin mosaya da yake da su a tsakanin matasa masu sa jar hula zai taka rawar gani a wannan zabe mai zuwa.
Sanata Kwankwaso an san shi da lissafin siyasa. Mutum ne da mutane suke son sa saboda kishin kasarsa da kwarin gwiwa da jajircewa da ji da kansa. Tsawon shekaru ya tabbatar da shi jajirtaccen dan siyasa ne.
Kwankwaso cikakken dan siyasa ne wanda ya shafe shekara 30 a cikinta, inda ya samu nasarar kaiwa kololuwa a siyasa a watan Yunin 2022 lokacin da a karon farko ya samu takarar Shugaban kasa, duk da cewa wannan ba shi ne karon farko da ya yi yunkurin hakan ba.
Idan za a iya tunawa yayin rantsar da shi a karo na biyu a matsayin Gwamna a ranar 29 ga Mayun 2011, Kwankwaso ya umarci magoya bayansa su sa fararen kaya da jar hula, lamarin da ya haifar da sa jar hula wadda alama ce ta tsarin Kwankwasiyya.
A shekarar 2014 bayan ya shiga majar Jam’iyyar APC ya yi takara da Shugaba Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar. A zaben-fid-da-gwanin da aka gudanar a Jihar Legas, Kwankwaso ya zo na biyu, inda ya samu kuri’a 974, yayin da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zo na uku da kuri’a 954.
kokarin da ya yi a zaben-fid-da-gwanin ya kara masa shahara a siyasar kasar nan. Haka kuma, a 2018 bayan ya dawo Jam’iyyar PDP, ya sake tsayawa takarar Shugaban kasa, inda tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya kayar da shi.
Cikakken dan siyasa
’Yan makarantarsu da abokan aikinsa sukan tuna kuruciyarsa da yaron kauye mai kwarin gwiya na musamman da kuma dogon buri. Ya kasance matashi kaifi daya wanda ke sa gabansa duk inda ya dosa.
Abokansa da abokan siyarsa suna bayyana shi da mai cim ma buri, ’yan makarantarsu sun ce tuntuni ya nuna bukatarsa ta shiga siyasa, sannan ya nuna siffofin shugabanci a lokacin da yake dalibta a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna Polytechnic, inda ya yi nazarin injiniyar gyaran famfo/bututu.
Alhaji Ahmad Rabi’u wanda Kwankwaso ke gaba da shi a Kaduna Polytechnic ya ce, ‘‘Akwai lokacin da aka yi tsaikon biyan mu kudade daga Kano. Kwankwaso ne ya bugi kirji tare da wasu mutum hudu domin bibiya. Suna dawowa aka turo wakilai daga Kano domin biyan mu alawus din da muke bi. Haka ya sa mu cikin farin ciki a wancan lokaci. Koyaushe yakan shige gaba a irin wadannan matsaloli.”
A matsayin Kwankwaso na Gwamnan jihar da ta fi yawan al’umma daga 1999 zuwa 2003 da 2011 zuwa 2015 ya aiwatar da manufofin da suka inganta rayuwar mutane, kamar ciyar da daliban makarantun gwamnati da koya wa mata sana’a da kuma ba matasa jari. Wannan shi ya ba shi farin jini a lokacin da yake mulki da bayan barin mulki.
Kwankwaso kwararren dan siyasa ne a siyasar Najeriya, inda ya yi dan Majalisar Wakilai, ya yi Gwamna, ya yi Minista, sannan ya yi Sanata.
Wannan ya sa yake son yin alfahari da hakan a duk lokacin da ya samu dama. Ya cancanci yin hakan.
Fara siyasa
Siyasar Kwankwaso ta samo asali ne tun lokacin da yake dalibi, inda ya rike mukamin Mataimakin Sakatare Janar na kungiyar daliban Jihar Kano, sannan ya rike Shugaban kungiyar dalibai ’Yan Jihar Kano reshen Kaduna Polytechnic. Haka kuma ya yi mamba na hukumar gudanarwa ta Tsangayar Koyar da Aikin Gona da kuma Tsangayar Manyan dalibai ta Jami’ar Nottingham da ke Ingila.
Ya fara siyasarsa ta jam’iyya ne a lokacin da aka zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Madobi (a 1992). Ya rike mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, mukamin da ya fito da shi fili a siyasar kasa.
Sai dai bai jima ba a mukamin sakamakon juyin mulkin soja. A 1994 an zabi Kwankwaso wakili a Taron Tsara Kundin Mulki kasa wanda ya sahare wa Jamhuriya ta Hudu hanya.
A wannan jamhuriyya, ya tsaya takara, inda ya zama Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003. A lokacin mukinsa Kano ta samu gagarumin ci-gaba. An nada shi Ministan Tsaro a 2003 zuwa 2006. Tsakannin 2006 zuwa 2007 Kwankwaso ya zama Mashawarci na Musamman ga Shugaban kasa kan Yankin Dafur/Somaliya.
Haka kuma daga 2009 zuwa 2010 ya wakilci Arewa maso Yamma a Hukumar Gudanarwar Hukumar Raya Yankin Neja Delta, inda daga bisani ya ajiye mukamin bisa kashin kansa.
Saboda kishin kasar da ke ransa, Kwankwaso ya sake tsayawa takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Afrilun 2011, inda ya kayar da Jam’iyyar ANPP da Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta.
Wannan nasara ta sa ya bar tarihi na dawowa kujerar Gwamna bayan shekara takwas. An haifi Muhammad Rabi’u Musa a ranar 21 ga Oktoba, 1957 a garin Kwankwaso da ke karamar Hukummar Madobi a Jihar Kano.
Kwankwaso ya taka matakai daban-daban kafin ya kai kokoluwa a siyasa. Shafinsa na Dandalin Sada Zumunta ya bayyana cewa, ya fara makaranta yana da shekara hudu, inda aka sa shi a makarantar allo, bayan shekara biyu ya fara makarantar boko a firamaren garin Kwankwaso daga 1962 zuwa 1969.
Bayan nan ya shiga Makarantar Koyar da Sana’o’i ta Wudil Craft School daga 1970 zuwa 1972, sai kuma Kwalejin Kano Technical and Training School daga 1972 zuwa 1975.
Daga bisani ya wuce zuwa Kaduna Polytechnic daga 1975 zuwa 1980, inda bayan ya kamamala ya shige karo karatu a Middlesed Polytechnic da ke Ingila da (1982-1983) sai Jami’ar Loughborough Unibersity of Technology (1982-1985) da kuma Nottingham University (1987- 1991) duk a Ingila.
Daga baya ya yi kwas a Derby National Water Council (1982) da Derby Water Industrial Training (1985) da London Industrial Training (1985).
Kwankwaso ya fara aiki a Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano (WRECA), inda ya fara da matsayin Jami’in Kula da Gyaran Famfo/Bututu zuwa matsayin babban injiniya. Ya rike mukamai iri-iri a wurare daban-daban, kamar Jam’in Kula da Samar da Ruwa a Cikin Birni da Manajan Ayyuka a dam din Goje da kuma Jami’in Bincike a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
Alhaji Ibrahim daya ne daga cikin abokan Kwankwaso na yarinta kuma makusancinsa, ya ce, ‘‘Yana matukar kula da kuma girmama abokantaka. Ya yi yunkurin shigo da ni siyasa, amma na ki, duk da haka yana haba-haba da ni. Yana ba ni amsa a duk lokacin da na tura masa sako ta waya, sannan yakan tsaya mu gaisa a duk inda ya gan ni.’’
Sabon salon kamfe
A yayin da ragowar ’yan takarar Shugaban kasa suke mayar da hankali a manyan birane domin ganawa da masu zabe, shi kuwa Kwankwaso yana shiga kananan hukumomi ne domin gananawa da masu zabe a garuruwansu. Shugaban Jam’iyyar NNPP, Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali ya ce, a yanzu ayarin kamfe na Shugaban darikar Kwankwasiyya ya shiga kananan hukumomi 650 don ganawa kaitsaye da masu zabe.
Haka kuma, kafin zabe za su zaga kananan hukumomi 774 na kasar nan. A wata hira da aka yi da shi ya ce, ‘‘Muna so mu gana da ’yan Najeriya kai-tsaye a garuruwansu domin sanin bukatunsu da kuma gaya musu abin da muka shirya yi wa kasar nan idan aka zabe mu.’’
A lokacin da ya ziyarci basaraken gargajiya, Och’Idoma, Dokta. John Elaigwu Odogbo a Otukpo da ke Jihar Benuwai, ya shida masa cewa, ’yan Najeriya suna bukatar mutum kamarsa a matsayin Shugaban kasa, wanda ya samar wa al’umma romon dimokuradiyya a baya.
Ya tsaya iya Kano
A lokacin da Kwankwaso ke ratsa lungu da sako na kasar nan don tallata takararsa masana cewa suke kamata ya yi ya mayar da hankali wajen ganin ya samu nasarar lashe zaben Gwamna a jihohin Kano da Jigawa da sauran jihohin Arewa maso Yamma domin karfafa tushen siyasarsa kafin zaben gaba.
A cewar wani manazarci, kamata ya yi Kwankwaso ya yi koyi da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Tinubu wanda bayan kammala wa’adinsa na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Legas, sai da ya tabbatar da cewa ya fito da magajinsa, ya kuma tabbatar da ya kafa duga-dugansa a dukkan sassan shiyyar Kudu maso Yamma, kafin ya fito ya nemi takarar Shugaban kasa.
Daya daga cikinsa abokansa da suka zauna a Majalisar Dattawa a tsakanin (2015- 2019) ya bayyana Kwankwaso a matsayin gogaggen dan siyasa da a kullum yana goyon bayan talakawa, sai dai ya soki tsayawa takararsa ta neman Shugaban kasa.
Ya ce, idan ni ne shi, ba zan fito takarar Shugaban kasa ba. Zan ci gaba a zaman sanata, sannan ina tallata ’yan takarar Gwamna da na Majalisar Dattawa da na wakilai. Zan kasance na zama mai fada-a -ji a siyasar Kano. Wannan ya fi masa a kan wannan takarar ta Shugaban kasa wadda ba za ta kai shi ko’ina ba.
“Na tuna a lokacin da muke Majalisar Dattawa na yi kokarin ba shi shawarar cewa idan ni ne shi zan rike jihata in nuna karfina, inda wasu jam’iyyu za su zo don neman hadin gwiwa da ni. Za su ce ‘ka zo za mu mara maka baya a kan kujerunku na Gwamna da na ’yan majalisa, muna son ku kuma ku ba mu goyon bayan samun nasarar lashe zaben Shugaban kasa. Da hakan ya fi zama mai sauki sosai a gare shi,” in ji shi.
Sai dai wani jigo a Jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ce wancan batu an fada ne kawai, amma dai ya sani a dukkan ’yan takarar Shugaban kasa, Kwankwaso ne kadai ya fi cancantar ya shugabancin kasar nan babu ko shakka.
“Duka sauran ’yan takarar Shugaban kasar suna da matsala game da cancantarsu. Muna kalubalantarsu su gabatar da takardun shaidarsu, kuma dukkansu suna da kashi a duwawunsu, a dukkan wadanda suka yi aikin gwamnati, babu wanda ya kafa tarihi irinsa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati. Babu dayansu da ke kusa da shi, don ba a taba zarginsa da aikata wani laifi ba,” in ji shi.
Shi ma Farfesa Alkali ya ce, “Kwankwaso mutum ne mai jajircewa, kuma ko a lokacin da ya fara wannan yunkuri a shekarun baya, mutane da yawa sun tsorata da fitowar tasa.
“Yana da juriya, kuma koyaushe yana kokarin shawo kan duk wani kalubale da zai kawo masa cikas. Lokacin da muka fara wannan tafiya, yawancin mutane suna ganin ba za mu je ko’ina ba. Sun ce NNPP siyasar Kano ce kawai, amma daga baya sai suka mai da ita ta zama ta Arewa. To ga shi a yau, NNPP ta zama wani babban kalubale mai firgitarwa ga jam’iyyun biyu (APC da PDP) wadanda a yanzu suke tsoronta,” in ji shi.
Rigimar kudaden fansho
Duk da cewa an sha musantawa, cewa an yi ta samun takun-saka a kan karkatar da kudaden fansho a wa’adi na biyu na gwamnatin Kwankwaso abin dai ya ci gaba.
A wata takardar korafi da Barista Mustapha Danjuma, ya rubuta a madadin Injiniya Abubakar Maisha’ani da Alhaji Najumai Garba Kobo, a shekarar 2015, ’yan fanshon sun yi zargin cewa Kwankwaso ya karbi gudunmawar Naira miliyan 70 daga kowace karamar hukuma 44 da ke Jihar Kano, wanda adadin kudin ya kai jimillar Naira biliyan 3.08 domin zaben fid-da-gwani na neman takararsa ta Shugaban kasa a 2015.
A watan Oktoba, 2021, an samu rahotannin cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tuhumi tsohon Gwamnan kan karar da ’yan fansho suka shigar a gabanta.
Sai dai a lokacin da yake mayar da martani, daya daga cikin masu biyayya ga Kwankwaso, Aminu Abdulsalam, ya ce ’yan fansho a jihar da ke zargin tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso da zamba za su shiga wuta domin ba mutanen arziki ba ne.
Ya ce ’yan fanshon sun yi kuskure da suka kai karar Kwankwaso ga Hukumar EFCC saboda ya yi amfani da kudaden fensho ne, kamar yadda doka ta tanada.
Tallafin karatu da taimakon jama’a
A wa’adin mulkinsa na biyu, daruruwan dalibai ne ’ya’yan marasa galihu suka amfana da tallafin karatu na gwamnatinsa.
Domin ci gaba da shirin bayar da tallafin karatu bayan karewar wa’adinsa na biyu, Kwankwaso, ya ce ya sayar da kadarorinsa don ci gaba da ba da tallafin karatun.
Kwankwaso, wanda ya ce a koyaushe yana tsara wa kansa abin da zai yi don al’umma, ya ce sama da dalibai 3,000 ne suka ci gajiyar shirin bayar da tallafin karatu daga shekarar 2011 zuwa 2015 lokacin da ya rike da mukamin Gwamnan Jihar Kano.
Ya ce ya kirkiro gidauniyar ce don saka wa jama’a kan irin dimbin goyon bayan da suka ba shi a lokacin zabe a Jihar Kano.
Ya kara da cewa, “Lokacin da muka tallata ba da tallafin karatun a shekarar 2019, ’yan kalilan mutane muka samu da suke da digiri mai daraja ta daya, saboda tun a rukunin farko muka gama da masu daraja ta daya, haka masu digiri mai daraja ta biyu, su ma mun gama da su a Jihar Kano,” in ji shi.
Ta hanyar gidauniyarsa Kwankwaso ya taimaka wa dubban zawarawa su yi aure.
RMK 2023: Alkawurana ga ’yan Najeriya
A cikin littafin kudirorinsa mai shafi 160 da ke dauke da manufofinsa mai taken, “Alkawurana gare ku. Tsarin RMK2023.” Kwankwaso ya yi alkawarin samar da shugabanci bisa adalci, idan aka zabe shi.
Da yake karin haske, Kwankwaso ya ce; “Za mu yi jagoranci na kishin kasa, bisa kudurori bakwai na kawo ci gaban al’umma da suka hada da Bunkasa rayuwar jama’a, Rashin son kai, Mutunci, Adalci, Gaskiya da Jagoranci bisa misali. Za mu yi adalci ga kowa, kuma za mu tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki na mulki. Ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru don dawo da zaman lafiya da tabbatar da tsaro da hadin kai a karkashin abin da ya yi wa lakabi da “Tsaron rayuwar dan Adam.”
“Sannan za mu yi la’akari da tanadin sashe na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wanda ke cewa ’’Samar da tsaro da jin dadin jama’a su ne manyan manufar gwamnati,” za mu tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya da kuma yin aiki haikan don karfafa hadin kai a tsakanin ’yan Najeriya gaba daya.
“Rashin bin doka yana haifar da rashin zaman lafiya. Za mu tabbatar da cewa kasarmu tana bin doka da oda: sannan mulki na al’umma ne, dole ne mu kiyaye ka’idar cewa kowa daidai yake a gaban doka,” in ji shi.
Ga manyan ’yan kasa kuwa tsohon Gwamnan Jihar Kanon alkawari ya yi na abin da ya kira, “girmamawa da kulawa, inda ya kara da cewa, “ba za a yi watsi da manyan kasa ba, tsofaffin sojoji da ’yan fansho da suka bayar da gudunmawarsu da dukiyoyinsu suka hidimta wa kasa. Na yi alkawarin tabbatar da cewa wadanda suka yi ritaya sun samu rayuwa ta mutunci bayan sun bar aiki,” in ji shi.
Ya kuma yi alkawarin kare tsarin dimokuradiyya a dukkan matakai, ya ce zai goyi bayan dukkan cibiyoyin dimokuradiyya don tabbatar da ci gaba a tsarin siyasa, da dorewar zaman lafiya a kasa.
“Za kuma mu kafa, kwamitocin ci gaban al’umma gundumomi zabe 8,809, don sake farfado da su don su kara kokarin gwamnati na tabbatar da ta shigar da al’umma cikin harkokin mulki. Wannan zai zama silar gwajin da aka yi na tsawon shekara takwas a Jihar Kano a lokacin mulkinmu,” inji shi.
Dangane da alaka da kasashen waje kuwa cewa ya yi “Za mu ci gaba da yin hadin gwiwa cikin lumana da kwanciayar hankali don samun cin moriyar alakar da ke tsakanin kasashenmu da sauran gwamnatocin kasashe, za kuma mu sake fasalin manufofinmu na ketare don nuna matsayinmu na zama uwa a Yammacin Afirka da Afirka baki daya da kuma dawo da martabar kasarmu a idon duniya.”
Ya kuma yi alkawarin kawo sauyi kan harkar noma ta hanyar sa hannun jari a fannin fasahar zamani da bayar da horo don samun wadatar abinci a kasa da kuma nahiyar Afirka gaba dayanta.
“Mun yi alkawarin tabbatar da ingantattun ayyuka ta hanyar inganta gandun daji, noma, kiwo, kiwon kaji da kifi da kuma tabbatar da daga darajar noma da kare manoma da masu kiwo da kuma jama’ar masu amfani da su,” in ji shi.
Shin yaya nasarar da madugun tafiyar jar hula za ta kasance a zaben na gobe Asabar? Shin zai ba mara da kunya ko a’a? Duka wadannan masu jefa kuri’a kusan miliyan 93.46 ne za su tantance a ranar Asabar.