Akwai abubuwa da dama wadanda suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya.
Kaushin kafa yana fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar: Yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi.
Akwai nau’o’in mai da dama wadanda ake sayar da su domin magance matsalolin kaushin fata, amma yawancinsu suna da tsada.
Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da zan lissafo muku.
- A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.
- Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki, sannan suna sa fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki, sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku kafin a wanke.
- Za a iya kwaba fiya, sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga cikin jiki.
- A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya danyi dumi sannan a mulke fatar jiki kaf da shi, na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka a kullum.
- Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum yana taimaka wa fata sosai.
- A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.
- A samu ayaba da nono ko kindirmo sannan a kwaba a waje daya, a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20, sannan a wanke da ruwan dumi.
- A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, yin amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.
- A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bari na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.