✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalelenku: Sabbin bidiyon Safara’u sun fara tayar da kura

Bidiyon dai sun yi ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

Jaruma Safiya Ahmad, wadda aka fi sani da Safara’u Kwana 90 ta sake tayar da kura a kafofin sadarwa bayan ta fitar da wasu bidiyo na wakoki tana rawa.

Jarumar wadda ta fara haskawa a shirin Kwana 90 na Arewa24 mai dogon zango ta dade tana tayar da kura a kafofin sadarwa tun bayan cire ta daga fim din.

Idan ba a manta ba, an cire ta ne a shirin na Kwana 90 bayan bidiyon tsiraicinta ya bayyana a kafofin sadarwar.

A wata tattaunawarta da Aminiya, jarumar ta ce ba wai bidiyon tsiraicin ba ne ya sa aka daina ganin ta a shirin
Kwana 90, inda ta ce, “Lokacin da ake ci gaba da daukar shirin ne na kwanta rashin lafiya.

Sun fara aiki, ni kuma ina kwance ba ni da lafiya, don haka ne a lokacin suka ga ba za su iya jira na ba, sai suka dauko wata ta ci gaba a matsayina domin a
gaskiya a lokacin ba zan iya yin aiki ba domin ba ni da lafiya sosai.”

A game da bidiyon kuwa cewa ta yi, “Na
shiga damuwa sosai, amma ban nuna wa kowa ba, kuma ban ce komai ba. Abin da ya zo min zuciya shi ne, akwai alamar zan samu daukaka a gaba shi ne hakan ya faru.”

Tun daga nan aka daina jin duriyarta,
sai daga baya ta koma yin fim a Kafawood ta Kaduna, inda ta yi wani
fim mai suna Kaddarar So.

Bayan an kwana biyu ba a ji ta ba, sai aka fara ganin kananan bidiyonta
tana wakar kwalele, tana rawa, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce da zage-zage, inda wasu suke cewa tana batsa ne kuma tana nuna jikinta a bidiyon.

Sai dai ko a jikinta, domin ci gaba ma take da sako sababbin bidiyon.

%d bloggers like this: