✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ta kori malami saboda badala da daliba

Hukumar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ta sallami wani shugaban tsangayar koyar da ilimin Injiniya, Danjuma Alhassan a kan zargin cin zarafin wata daliba…

Hukumar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ta sallami wani shugaban tsangayar koyar da ilimin Injiniya, Danjuma Alhassan a kan zargin cin zarafin wata daliba a makarantar. 

Kwalejin ta amince da a sallamar malamin ne daga makarantar, bayan zaman taron hukumar kwalejin karo na 91 da aka yi ranar 30 Janairu 2020.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun ‎mataimakin Magatakardar Kwalejin Samuel Y. Obochi, ‎wanda ya sanya hannu a madadin Magatakardar Kwalejin kuma jaridar Aminiya ta samu kofin takardar.

A cewar takardar dalibarce ta kai kara inda kuma aka nemi shi malamin da ya bayyana a gaban hukumar sannan ya yi hakan, daga bisani aka tabbatar da ceawa ya aikata laifin.

Shugaban makarantar Farfesa Idris Bugaje, a kwanakin baya ‎an yi gargadin cewa Kwalejin ba zata amince da cin zarafin dalibanta ba dan haka ya nemi a kiyaye dokar.