Hukumar Gudanarwar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Kano, ta sanar da ranar Litinin 2 ga watan Nubamba a matsayin ranar komawa karatu kamar yadda aka saba.
Jami’in Hulda da Jama’a na kwalejin, Auwal Mudi Yakasai, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a 23, ga watan Oktoba, 2020.
Sanarwar ta ce an bukaci dalibai da su kiyaye dokokin kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus.
Hukumar makarantar ta ce; komawa makarantar ya shafi dukkan dalibai masu karatun NCE da Pre NCE da NCE, Part-Time.