✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalara ta kashe mutane 214 a Malawi

Ta zama barkewar cuta mafi muni da kasar ta fuskanta cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Mutane 214 sun halaka sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a kasar Malawi inda hukumomi ke ci gaba da bin matakan dakile annobar.

Cutar wadda aka fi sani da Kwalara ta yi wannan mummunar ta’asa ce a Malawin kamar yadda Ma’aikatar Kula da Lafiya ta kasar ta tabbatar.

Cikin watan da ya gabata aka samu barkewar cutar, inda haka ya zama barkewar cuta mafi muni da kasar ta fuskanta cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Hukumomi sun tabbatar da cewa akwai sabbin kamuwa da cutar kusan mutane 180, kuma yanzu haka cutar tana lafawa.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna damuwa game da barkewar cutar ta amai da gudawa da aka samu a kasar ta Malawi, inda hukumar tare da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, suka yi riga kafin cutar ga yara kusan milyan uku a kasar.

Kasar ta Malami da ke yankin Kudancin Afirka tana sahun gaba na kasashe masu tasowa da ke cikin matsanancin talauci.