Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan dabar da suka balle gidajen yari biyu a jihar Edo ranar Litinin sun kubutar da fursunoni 1,993.
Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Cikin Gida, Mohammed Manga, ya bayyana haka a wata takardar sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Manga ya ce mutanen da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki ne gidajen yarin, inda suka saki fursunonin sannan suka saci bindigogi biyar a dakin ajiye makamai na ofishin ‘yan sandan da ke yankin.
Mohammed ya ce ‘yan sanda sun tabbatar da kama mutum 12 da ke da alaka da harin, kuma sun kwato bindigogin biyar.
Takardar na dauke da bayani kamar haka: “Masu zanga-zangar #EndSARS sun kai hari a gidajen yari biyu da ke birnin Bini da kuma garin Oko na jihar Edo a ranar Litinin.
“Sun kubutar da fursunoni wadanda adadin su, a kirgar karshe da aka yi, ya kai 1,993, kafin su yi sata har da makaman da ke a dakin ajiya”.
Ya kara da cewa, “‘Yan dabar sun zo ne da yawa dauke da muggan makamai suka afka wa ma’aikatanmu da ke tsaron gidajen yarin.
“Sun zo ne da niyyar su balle gidan kason domin kubutar da fursunonin, da kuma yin sace-sace”.
Gwamnatin tarayya ta ce lamura sun lafa, sannan kuma an tsananta matakan tsaro a gidajen yarin da ke kasar nan.