Wani kunkuru mai kai biyu mai suna Janus ya yi bikin cika shekara 25 a duniya a ranar Lahadin da ta gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters wanda ya ruwaito labarin ya bayyana yadda mai kunkuru Misis Angelica Bourgoin ta taba bayan kunkurun a hankali da biro inda kawunansa biyu suka fito domin fara shirin bikin cikarsa shekara 25.
Kunkuru Janus yana da zukata biyu da huhu biyu, inda aka yanke kaunar zai yi dogon rai, saboda ba zai iya mayar da kawunansa biyu cikin kokon jikins don kauce wa masu kai masa harin cutarwa ba.
Kunkurun wanda aka fafe shi a Gidan Namun Daji na Geneba (Janiba) kasar Switzerland a 1997, Misis Bourgoin da abokan aikinta masu kula da dabbobi – suna da yakinin shi ne kunkuru mai kai biyu mafi tsufa a duniya – kuma zai iya kula da kansa.
Suna ciyar da shi da salad da aka samar ta amfani da takin gargajiya, kuma suna yi masa tausa da wanka a kullum.
Kuma sukan taimaka masa wajen motsa jiki ta yin tafiya da shi a-kai-a-kai wani lokaci ma tare da sanya masa kade-kade ko dora shi a kan keken katako mai taya.
“Ina jin saboda kulawar da muke ba shi da sadaukar da kanmu ya sa har yanzu yake raye,” inji Bourgion.
Janus, kunkurun kasar Girka ne da aka sanya wa sunan wani gunkin Rumawa mai kai biyu, inda za a yi masa biki na musamman a karshen wannan mako.