✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ‘Yan Gwari ta yaba wa Gwamna Masari

kungiyar Masu Sana’ar Sayar da Kayan Miya da aka fi sanir da ‘Yan Gwari ta Jahar Katsina sun ce komawarsu sabon wurin da aka ba…

kungiyar Masu Sana’ar Sayar da Kayan Miya da aka fi sanir da ‘Yan Gwari ta Jahar Katsina sun ce komawarsu sabon wurin da aka ba su na din-din-din domin tafiyar da harkokin kasuwancinsu ya zamo masu wani karin cigaban da ba su yi zato ba. 

Shugaban kungiyar ‘Yan Gwarin, Alhaji Babangida Hussaini Kaita ne ya shaidawa Aminiya haka a lokacin da wakilinmu ya ziyarci sabuwar kasuwar da aka mayar da masu sana’ar sayar da kayan miyan, wadanda aka maido su a wannan waje nasu. Kamar yadda shugaban ya ce, “A gaskiya a yanzu mun samu natsuwa tare da karin cigaban harkokin kasuwancinmu. Da ma can inda muke a babbar kasuwa wato Santara Maket wuri ne na aro, domin an fidda wannan fili don ajiye motocin masu shiga kasuwa. To mu kungiya mu muka nemi a ba mu filin da zamu zauna tun a lokacin, amma abin bai tabbata ba sosai sai a lokacin wannan gwamnati ta Aminu Masari. Bayan kungiya ta gyara filin da ada daji ne, mun kuma roki wasu abubuwa na more rayuwa wadanda mun samu wasu, wasu kuma muna jiran samun su nan bada jimawa ba da yardar Allah”. 

Daga cikin irin abubuwan da shugaban ya ce sun samu har da rijiyoyin burtsatse guda biyu wadda Gwamna ya sa hukumar RUWASSA ta gina masu, tankuna ajiye ruwa guda shida masu cin lita 400, bayan duk inda ya kamata a ja kan fanfo an ja, kuma ruwa na zubowa. Kazalika gwamnatin Masarin ta ba su injinan kawo hasken wutar lantarki guda, domin janyo ruwa da kuma samun haske a cikin kasuwar, wadda take matattara ce ta masu wannan sana’a a ciki da kuma wajen jahar.

Alhaji Babangida Kaita ya ce, “Daga cikin abubuwan da muke jiran gani daga gwamnati sun hada da hanyoyin da za su ratso cikin kasuwar domin samun saukin shigowar motoci masu kawo ma na kaya da kuma magudanan ruwa. Dukkan wadannan bukatu namu nan take Mai girma Gwamna Masari ya bayar da umarnin aiwatar da wadannan ayyuka a lokacin da ya kawo mana ziyarar ba-zata a lokacin da muke ta shirye-shiryen zamanmu a kasuwar”. 

Da ya juya akan irin ayyukan da kungiyar ta yi na ganin sabuwar kasuwar ta su ta inganta, shugaban ya ce, baya ga gyaran filin har ila yau kungiya ta rarraba rumfuna ga masu wannan sana’ar. Ta kuma raba rumfunan ne ta hanyar bayar da rumfar ga duk wani wanda yake da rumfa tsohon wurin da suka taso. Bayan ganin cewa an ba duk wani mai rumfa rumfarsa, sannan daga baya kungiya ta ci gaba da bayarwa ga wadanda ba su da rumfunan, wadanda ko dai suna rabe ne a rumfar wani ko kuma suna amfani da lema a wajen gudanar da sana’o’in nasu. Anan shugaban ya karyata zargin da wasu ke yi na cewa, ana ba wasu rumfuna daga waje. 

Kazalika shugaba Babangida ya ce, “Mun fitar da wurin da zamu gina ofishin kungiya da masallaci da wajen Bahaya wadanda tuni aikinsu ya yi nisa”. Kamar dai yadda Aminiya ta lura a wannan sabuwar kasuwar ‘Yan Gwari cewar ba su kadai ba ne suke amfana da ita, hatta da masu gidajen buga bulo, kafintoci, masu acaba, sayar da abinci da sauran wasu nau’o’in sana’un suna samun ciniki sosai. Malam Idris mai sana’ar yin faci ya ce, shi kam gwamma da aka yi domin sana’arsa ta faci ta inganta.

A can bangaren masu sayar da Rake kuwa, shugaban kungiyar tasu Malam Yakubu Duba ya ce, “A can inda muke muna kuntace saboda mota biyu ba ta iya tsayawa a lokaci guda don sauke kaya, amma yanzu dubi fili wanda mota bakwai ma ta iya tsayawa. Mu kam gaskiya mu da Gwamnatin Masari sai addu’ar fatan alheri”. Shi dai anan ya ce, sun bi duk hanyoyin da suka kamata don rabawa mutanansu rumfuna. 

Kazalika,su ma an yi masu rijiyar burtsatse tare da ba su injinan samar da wutar lantarki don tara ruwa a cikin tankunan da aka sanya masu. Sai dai kuma dukkan shugabannin sun ce za su bayar da duk wata gudunmuwar da za su iya domin ganin gwamnatin jahar ta cigaba da ayyukan alherin da ta sa a gaba. Sun kuma shawarci mabiyansu da su zamo masu bin doka da oda tare da zama masu da’a da kuma taimakon juna.