Shugaban Kungiyar Matasa da Wayar da kan Jama’a ta Mashaya Youth Mobilization, Alhaji Umaru Sanda Ambursa ya yi kira ga al’ummar jihohin kasar nan 29 da za a gudanar da zabubbukan gwamnoni da wakilan majalisun dokoki su gudanar da zabubbukan cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yadda aka gudanar da na Shugaban Kasa da na ’Majalisar Tarayya cikin kwanciyar hankali da lumana.
Alhaji Umaru Sanda Ambursa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
Shugaban ya ce aikin kungiyar shi ne wayar da kan jama’a a kan abin da ya shige musu duhu musamman a wajen gudanar da zabe da kuma fadakar da jama’a a kan zaman lafiya da kuma zaben shugabanni nagari domin ci gaban al’ummar Jihar Kebbi da kasa baki daya.
Alhaji Umaru Sanda Ambursa ya ce ya kamata jama’a su yi amfani da darussan da suka samu daga zabubukan da suka gudana a baya wajen daukar matakan da suka dace na gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ya yi kira ga jama’a su rika yin watsi da jita-jita da maganganun da ka iya haifar da fitina a cikin al’umma.
A karshe ya ce, “Ina kira ga ’yan jarida su ci gaba da watsa alheri da abin da zai tabbatar da zaman lafiya a kasarmu.”