✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Sure Start ta wayar da kan mata kan tsafta lokacin al’ada

kungiyar Sure Start Initiatibe ta bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta wadata makarantun ‘yan mata da bandakuna tare da samar musu da wadataccen ruwa don…

kungiyar Sure Start Initiatibe ta bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta wadata makarantun ‘yan mata da bandakuna tare da samar musu da wadataccen ruwa don tsaftace kansu a lokacin da suke cikin kwanakin al’ada.

 Shugabar kungiyar Hajiya Binta Shehu Bamalli ce ta yi wannan kira a yayin da kungiyar ta gudanar da gangamim wayar da kan mata a kan muhimamncin tsafta lokacin al’ada domin bikin zagayowar ranar ‘ya’ya mata ta duniya wanda aka yi a makon da ya gabata.

Hajiya Binta Bamalli ta koka da yadda ilimin ‘ya’ya mata ke samun cikas saboda rashin yanayin da za su kula da kansu a lokacin al’ada “wasu yara matan saboda rashin yanayi mai kyau, ba bandaki ba ruwa sukan daina zuwa makaranta har sai sun kammala al’adarsu wanda hakan ba karamin cikas ba ne ga iliminsu ko, kuma a wasu lokutan yanayin da suke ciki na damuwa na haifar musu da rashin natsuwa a aji ballantana su fahimci abin da malami ke koyarwa. Wannan ya sa muka kafa wannan kungiya domin mu tabbatar an samar wa mata yanayi mai kyau wanda zai taimaka wa karatunsu, yadda za su sami natsuwa da kwanciyar hankali har su gane tare da fahimtar abin da malamansu ke koya musu”.

Har ila yau Hajiya Binta ta bayyana cewa baya ga batun ilimin yara matan, kungiyarsu na kokarin wayar da kan ‘yan mata game da yadda ya kamata su rika kula da tsaftar kansu yayin da suke al’ada, kancewar idan ba su kula da tsafta, akwai yiyuwar su hadu da wasu cututtuka wadanda ba su bayyana sai sun girma “muna so ‘yan mata su fahimci cewa idan ba sa yin tsafta lokacin al’ada akwai wasu cututtuka da ke shiga jikin mace wanda ke haifar da matsaloli bayan sun kara girma, domin sukan jawo rashin haihuwa da kaikayi da kuraje da sauransu” Inji ta.

Hajiya Binta ta yi kira ga gwamnati da ta fitar da wani tsari don gyaran bandakunan makaranun ‘yan mata. “idan son samu ne, gwamnati ta yi wani tsari ko da jadawali ta yadda za ta rika daukar makarantun ‘yan mata misali guda daya a kowane wata ta gyara musu bandakuna, ta samar musu da ruwa da kwandunan zuba shara. Na san abin zai dau lokaci mai tsawo kafin a kamamla amma dai na san abu ne mai yiyuwa. Mu ba mu son a ba mu komai amma muna so a yi mana wannan taimako saboda ‘ya’yanmu su sami yanayi  mai kyau na karatu wanda zai taimaka su fahimci abin da ake koya musu”

Shi ma a makalar da ya gabatar a wajen taron Farfesa Malami Buba wanda malami ne a Jami’ar danfodiyo da ke Jihae Sakkwato, ya bayyana cewa ‘ya’ya mata da yawa ne ke fuskantar matsaloli a sha’anin karatunsu wanda hakan ke zama kalubale ga rayuwarsu. “kididdiga ta nuna cewa akwai alaka tsakanin samun makewayi a wurin yara mata da kuma harkar karatunsu. ’Yaya mata da  yawa suna fuskantar matsala a lokutan al’ada saboda rashin makewayi a makarantun da suke wanda hakan ke sa su daina zuwa makaranata na tsawon wadannan kwanaki. Idan har za a ci gaba da samun haka, akwai yiyuwar watarana yaran nan su rasa jarrabawa, wanda hakan ke nufin ci baya a harkar karatunsu.  Idan mun duba yawan rabin al’ummarmu a kasar nan mata ne, idan kuma ba su sami ilimi ba ka ga akwai matsala ke nan.”

Farfesa Malami ya yi kira ga gwamnati kamar yadda take daukar nauyin bayar da litattafai ga dalibai to ta dauki nauyin raba audugar mata ga ‘dalibai mata, kasancewar hakan zai bunkasa iliminsu. “kin san anan Arewa batun alada ba a tatatuna shi saboda kunya, don haka muke kira ga gwamnati ta rika samar da audugar nan kyauta ga dalibai mata kamar yadda take raba musu liattafai. Haka kuma kafin gwmanati ta yi tunanin karin ginin ajujuwa ya kamata ta sa a ranta cewa akwai dalibai mata da ke bukatar makewayi wanda ya dace da bukatarsu. Na tabbata idan har ‘ya’ya mata suka sami tsaftataccen bandaki da kuma audugarsu a hannunsu za su sami natsuwa tare da mayar da hankali  ga abin da ya shafi karatunsu. Akwai bukatar a tallafa wa mata da duk wani abu da zai habaka harkar karatunsu”

Mafiyawan dalibai matan da suka halarci wannan taron wayar da kai sun bayyana godiyarsu ga wannan kungiya dangane da kayayaykin da ta raba musu tare da daukar alwashin amfani da ilimin da suka samu a wajen taron.