✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar MOPPAN ta yafe wa Rahama Sadau

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano (MOPPAN) ta ce ta yafe wa fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka…

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano (MOPPAN) ta ce ta yafe wa fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka dakatar da ita daga fim kamar yadda BBC ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Isma’ila Na’abba Afakalla, ya shaida wa wakilin BBC cewa, "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".

Afakalla ya kara da cewa sun dauki wannan mataki ne bisa la’akari da gafarar da jarumar ta nemi a yi mata kwanakin baya.

A cewarsa, "Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al’umar da take ciki.

"Don haka a matsayinmu na ‘yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi", in ji shi.