✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Manoman Katarkawa ta koka kan kwace gonakin ’ya’yanta

Kungiyar Manoman Katarkawa a Karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu wajen dawo da musu gonakinsu da Karamar Hukumar…

Kungiyar Manoman Katarkawa a Karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu wajen dawo da musu gonakinsu da Karamar Hukumar Warawa ta kwace.                                                                                                                                              Shugaban kungiyar Alhaji Adamu Hotoro ya yi wannan korafi a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano, inda ya bayyana cewa karamar hukumar ta Warawa a karkashin shugabancin tsohon shugabanta Alhaji Ibrahim Danlasan ta sayar da wasu daga cikin gonakin nasu lamarin da ya tilas wa manoman daina yin noma na tsawon lokaci.

“A da kimanin manoma 273 ne ke noma wadannan gonaki mai fadin kadada 1,014 karkashin Hukumar NALDA, amma a yanzu ba su fi kashi 30 ne ke noma gonakin ba, sakamakon sayar da wasu gonakin da karamar hukumar ta yi. Zan iya cewa a yanzu manomanmu ba su yi noma ba na tsawon shekaru wannan kuma ya hada da noman rani da na damin,” inji shi.

Shugaban Kungiyar ya bayyana cewa “A 1990 Gwamnatin Tarayya ta fito da wani shiri na bunkasa kasa da abinci wanda ta damka shi ga Hukumar NALDA.”

A cewarsa sun yi duk iya kokarinsu wajen ganin gonakin sun dawo hannunsu amma abin ya gagara, kasancewar wadansu daga cikinsu sai da aka gurfanar da su a gaban kotu aka daure su a kan haka. “Mun bi kadin maganar nan, mun kai kukanmu gaba, amma har yanzu ba mu samu masu share mana hawaye ba. A kan haka wadansu daga cikinmu har dauri suka sha. Ga shi ba mu yin noman, amma mun rasa masu tausaya mana,” inji shi.

Shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Ministan Aikin Gona Cif Audu Ogbeh su shiga tsakani ta hanyar tilasta Karamar Hukumar Warawa ta dawo musu da gonakinsu, don a samu dorewar zaman lafiya a yankin.

Har ila yau kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa shugabancin da zai kula da rikon Hukumar NALDA don samun bunkasar harkar noma a fadin kasar nan.

“Idan har aka samu aka kafa Shugabannin Hukumar Gudanarwar Hukumar NALDA, hukumar za ta zama mai cin gashin kanta wanda hakan zai bayar da dama ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da suka shafi ayyukan gona a fadin kasar nan kamar yadda ta yi a baya,” inji shi.

Yayin da aka tuntubi Ko’odinetan Hukumar NALDA a Kano Malam Sani Hamza ya tabbatar wa Aminiya da labarin, inda ya ce ofishinsa ya rubuta takardar korafi ga Hedikwatar Hukumar ta Kasa a kan hakan kuma ya rarraraba ta ga Ofishin Hakimin Warawa da na DPO din ’yan sanda da ke yankin.

Sai dai yayin da aka tuntubi Alhaji Ibrahim Danlasan wanda kungiyar manoman ta yi kukan cewa a lokacin mulkinsa ne aka kwace gonakin, ya ce dama tun farko ba manoman aka damka wa gonakin kai-tsaye ba, a cewarsa an damka gonakin ne ga Hukumar NALDA bisa yarjejniyar za a karbi gonakin bayan shekara shida. “Lokacin da wa’adin karbar gonakin ya cika sai Karamar Hukuma ta fara karbar gonakin yayin da ta gano cewa har wadansu daga cikin manoman sun fara sayar da gonakin ga wadansu mutane,” inji shi.

Har ila yau tsohon Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa kafin ya bar mulki sai da ya rubuta wa Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Kasa takarda inda yake sanar da ita a kan batun karbar gonakin da karamar hukumar ta yi.