✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar Malamai ta yi addu’ar neman a yi zabe lafiya

Malaman sun gudanar da taron addu'ar ne don samun nasarar yin zabe mai zuwa cikin lumana.

Kungiyar Malaman Musulunci ta Yarbawa sun bukaci ’yan Najeriya da su yi addu’ar samun nasara a babban zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma na ranar 11 ga watan Maris.

Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan kammala addu’o’in da aka gudanar a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, tare da shugaban kungiyar, Sheikh Abdurrasheed Mayaleeke da babban sakataren kungiyar, Farfesa Olaiya Abideen Olaitan.

Sun bayyana cewar akwai bukatar sanya Najeriya cikin addu’a duba da yanayin da ake ciki.

“Mun taru a yau ne domin neman yardar Allah a kan zabe mai zuwa, mu yi addu’ar ganin an mika mulki cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Za mu ci gaba da gudanar da addu’o’i a manyan masallatai daban-daban na tsawon lokacin da ake shirin mika mulki,” in ji Olaitan.

Ya kuma bukaci ’yan siyasa da su bi doka, su guji furta kalaman da za su iya kawo cikas ga harkar zabe da kwanciyar hankali.

“Muna kuma kira ga masu zabe da su kara hakuri da shugabanni a dukkan matakai.

“Muna kara kira ga daukacin ’yan Najeriya da su fito su yi zabe don kawo sauyi daga halin da kasar nan ke ciki.”