✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Maharba za ta taimaka wajen yaki da masu sace mutane a Taraba

Kungiyar Maharba a Jihar Taraba ta ce a shirye take ta taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu sace mutane  da sauran masu aikata…

Kungiyar Maharba a Jihar Taraba ta ce a shirye take ta taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu sace mutane  da sauran masu aikata miyagun laifuka .

Shugaban Kungiyar na karamar hukumar Ardo-Kola,Mallam Suleiman Sunkani ya furta haka a a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya.

Yace yan Kungiyar ta Maharba ta kasance tana da rajista tare da  kai’doji wanda dole kowanne dan Kungiya ya bi.

Mallam Suleiman ya kara da cewa ayyukan yan Kungiyar a daji suke gudanarwa watau  harbin namun daji  wanda haka din yasa suka fi kowa sanin sirrin daji.

Shugaban Kungiyar maharban  ya bayyana cewa kasancewar masu satan mutane da sauran ayyukan laifi a daji suke boyewa maharba in sun sami yardar jami’an tsaro zasu taimaka wajen  tarwatsa masu  aikata miyagun  ayyuka dake boye a dazuka suna  cutar da Jama’a.

Ya ce ba dajin da maharba suke  tsoron shiga a kasar nan saboda haka bukatarsu ita ce gwamnati ta jawosu a  jika a saka su cikin harkar tsaro kamar yadda ya kamata.

Mallam Suleiman ya kara da cewa Kungiyar tana  da rassa a dukkan kananan hukumomin jihar wadanda a yanzu ke fuskantar matsalar satar mutane

Ya ce ’yan kungiyar a shirye suke su tallafawa jami’an tsaro don ganin an shawo kan matsalar aikata laifuka a Jihar  musamman satan mutane wanda ta hana jama’a walwala.

Shugaban Kungiyar na maharba ya bayyana cewa yan Kungiyar sun bayar da taimakon sun wajen yaki da yan Kungiyar Boko_Haram a shekarun baya saboda jihohin da  suka fuskanci matsalar Boko_Haram sun san irin taimakon da ’yan kungiyar maharba suka bayar a yaki da ’yan Boko_Haram.

Yace saboda haka a yanzu ma a shirye suke su bayar da gudunmawarsu wajen fuskantar matsalar tsaro a Jihar ta Taraba

Malam Suleiman ya ce abin da suke bukata shine gwamnati ta rika baiwa yan Kungiyar kudin alawus da daukan nauyin  yin masu jinya in sun sami raunuka a lokacin da suke fuskantar masu aikata laifuka.

Ya kara da cewa akwai bukatar a taimaka masu da ababan hawa domin shiga daji a lokutan da bukatar hakan ta taso.