Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA) reshen jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya hanzarta amincewa da dokar da Majalisar Dokokin jihar ta kafa a kan Inshorar Lafiya a jihar.
Shugaban Kungiyar Dokta Bulus Peter ne ya gabatar da bukatar hakan lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu jim kadan bayan kungiyar ta kammala taronta na shekara-shekara a otel din Ta’al da ke Lafiya.
Ya ce tuni majalisar ta shigar da kudirin dokar, inda yanzu ake jiran amincewar Gwamnan.
Ya ce kungiyar za ta ziyarci Gwamnan nan b ada dadewa ba don ta kara yi masa bayyani dangane da muhimmancin amincewa da dokar kuma tana so ya kafa wata hukuma da za ta rika sa ido wajen aiwatar da shirin a jihar. Ya ce ba shakka da zarar an fara aiwatar da shirin talakawa da masu hannu da shuni za su amfana matuka musamman wajen samun wadatattun magunguna da kulawar kwararrun likitoci a jihar yadda ya dace sabanin yadda lamarin yake a yanzu inda masu hannu da shuni ne kadai ke da damar samun ingantattu da wadatattun magunguna a asibitotin gwamnati.
Game da manufar wannan taro da kungiyar ke gudanarwa shekara-shekara a jihar, Shugaban ya ce suna yin amfani da damar wajen jan hankalin likitocin jihar baki daya dangane da muhimmanci da ke akwai na su rika kula da marasa lafiya yadda ya kamata, don wani bincike na musamman da kwararru a fannin kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewa idan likitoci suna kula tare da nuna soyayya ga marasa lafiya da ke asibitocinsu, hakan yakan jawo samun lafiya cikin sauri.
Ya kara da cewa sukan kuma yi amfani da taron wajen raba wa al’ummar jihar marasa lafiya musamman mata da yara kananan magunguna kyauta a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar da sauransu.