kungiyar kwallon zari-ruga ta kasa za ta kaddamar da kwamitin kwararrunta da masu horar da ’yan wasa na shiyyoyi hudu da ke kasar.
Za a yi bikin kaddamarwar ne a gobe Asabar a dakin taro da ke filin wasa na kasa a jihar Legas bayan an yi taron karawa juna sani na kwanaki biyu wanda za a fara yau Juma’a 30 ga watan Janairu.
Sakatare Janar na wasan zari-ruga na kasa, Kehinde Laniyan ya bayyana cewa ana sa ran halartar daukacin membobin kungiyar a wurin taron.
‘Ya zama wajibi daukacin jami’ai kwararru da membobin kwamiti na kasa na kungiyar kwallon zari-ruga na kasa su halarci taron. Saboda taron wani babban ci gaba ne ga kungiyar da kuma harkar wasanni a kasa baki daya’. Inji shi.
Ya ce ‘Taron kara wa juna sani da za a gudanar za a yi ne don bunkasa wasan da kuma fadakar da jama’a kan harkar wasanni a Najeriya. Taron kara wa juna sanin zai mayar da hankali ne wajen tantance irin kwarewa da za a samu wajen bunkasa ’yan wasa ta hanyar bayar da horo a makarantu da shiyyoyi da kuma kasa baki daya’.
Ya kara da cewa ‘Taron karawa juna sanin an shirya shi ne don a fadakar da mahalarta taron cewa sashen kwararru shi ne zuciyar kungiyoyin wasanni saboda haka dole a ba shi kulawa ta musamman’.
Shugaban kungiyar kwallon zari-ruga na kasa bictor Fingesi shi ne zai gabatar da jawabi na musamman a wurin taron.
Wadanda kuma za su gabatar da kasidu sun hada da shugaban rediyon Brila FM Izamoje da shugaban kamfanin Hotsport na kasa da kasa da kuma kwararre a harkar wasanni Taye Ige.