✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Katsinawa Mazauna Legas na yi wa ’ya’yanta katin shaida

    kungiyar Katsina Mazuna Jihar Legas  ta umurci ’yan asalin jihar ta Katsina mazauna Legas da kowa ya samu katin shaidar cewa shi dan…

 

 

kungiyar Katsina Mazuna Jihar Legas  ta umurci ’yan asalin jihar ta Katsina mazauna Legas da kowa ya samu katin shaidar cewa shi dan jihar Katsina ne domin guje wa wulakanci daga  jami’an tsaro ko jami’an jiha ko kuma na gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar na Jihar Legas, Alhaji Abubakar Sanusi Faskari ya ce sun ba da wannan umurnin  ne biyo  bayan halin tsaro  da kasar ke fama da shi  kuma  hakan yana taimakawa, domin da  katin ne mutanensu suka tsallake kame ko wulakanci iri daban-daban a duk  fadin jihar har ma da jihohi makwabta.
Ya ce da farko wasu daga cikinsu ba su dauki wannan shawarar da muhimmanci ba, sai da wadanda suka yi suke fada musu amfaninta. “Mun samar da wannan tsarin ne domin ta haka kadai za a samu  saukin tantance  mutanen jihar  da kuma wace  irin sana’a  mutun ke yi kuma daga wace karamar hukuma yake a jihar ta Katsina.
Shugaban ya ce sun tsara  abin ne unguwa-unguwa kana sai an tantance ka an samu wadanda suka sanka kuma suke da tabbacin kai dan jihar Katsina  ne kana a ba ka katin shaidar, wanda ake  biyan yadda mutanen kowace unguwa suka tsara a kansa.
Ya ce  bayanan da ke kunshe a katin, wanda ke da  tsari iri guda, sun kunshi suna; karamar hukumar da ka fito; unguwar da kake a Legas, sai kuma sa hannun shugaba.
Taron, wanda suka yi shi a gidan  mallakar gwamnatin  Jihar Katsina da ke  kan titin Kofo Abayomi da ke unguwar bictoria Island, ya samu halarcin wakilai daga daukacin unguwannin da ke fadin jihar.