✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar IMAN ta tallafa wa marasa lafiya 3000

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya Musulmi (IMAN) ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, ta fara bikin makon kiwon lafiya na bana a…

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya Musulmi (IMAN) ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, ta fara bikin makon kiwon lafiya na bana a ranar Asabar da ta gabata a garin Wucicciri da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Kungiyar ta duba  marasa lafiya dubu uku, daga cikinsu akwai mutum 90 da aka yi musu tiyatar cututtuka daban-daban, inda aka yi  wa mutum 35 aikin ido kyauta.

Hatta dabbobi ba a barsu a baya ba a wannan shiri, inda likitocin dabbobi suka duba shanu da tumaki da awaki da jakuna da karnuka da kaji da sauran dabbobi. Kuma dukan aiki da magungunan da suka bayar kyauta ne domin nuna jinkai ga marasa galihu.

Haka kuma kimanin almajirai 300 da suka fito daga tsangayar Alaramma Abubakar Dauda da ke Hayin Katsinawa a garin Shika ne suka samu rigunan sanyi da magunguna da abinci tare da ba su shawarwarin yadda za su kasance cikin tsabta da rayuwa mai inganci.

Da yake nuna jin dadinsa Alaramma Abubakar Dauda wanda aka fi sani da Mai Almajire Hayin Katsinawa ya ce, “Na yi farin ciki da murna da wadannan baki namu duk da dai ba baki ba ne a wannan tsangaya tamu. Domin wannan ne karo na biyu da wadannan bayin Allah suka kawo wa almajiraina tallafi tare da duba lafiyarsu, kuma a wancan karo da suka kawo mana tallafi bayan sun tafi mun ga amfanin ziyarar tasu da kuma shawarwarin da suka bai wa dalibanmu. Don haka muna godiya ga Allah da kuma yi musu fatan alheri.”

A lokacin bude gangamin duba lafiyar jama’ar da ya gudana a Wucicciri, tsohon Daraktan mulki na Asibitin ABUTH, Barista Is’hak Bello, Wakilin Yarbawan Zazzau ya bayyana shirin da cewa, ceto rayukan marasa galihu da suke yankunan karkara wadanda ba su da karfi ko hikimar rabuwa da kananan cututtukan da ke jikinsu a tsawan lokaci saboda rashin hali abin yabo ne kwarai.

 Likitocin dabbobi a yayin aikinsu wajen shirin
Likitocin dabbobi a yayin aikinsu wajen shirin

Daraktan Kula da Shirin kuma Sakataran Kungiyar, Dokta Muhammad Mustapha Yakubu ya nuna gamsuwarsa kan yadda masu dauke da cututtuka a jikinsu suka bayyana domin cin gajiyar shirin.

Ya ce “Wannan shi ne karo na biyar da suke gudanar da irin wannan ba da tallafin kiwon lafiya, amma sai dai wannan karon ya sha bamban da lokutan baya, domin wannan karon mun duba mutane tare da dabbobinsu ne baki daya, kuma mun samu gamsuwa da yadda ma’aikatanmu suka gudanar da aikin da suka hada da samar da magunguna tare da yi wa mutane fida a kan lalurorin da suke damunsu har muka kai ga nasara,” inji shi.