✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar guragu ta Kuros Riba United tana neman tallafi

Duk da kasancewa ita taz o ta biyu a gasar wasan kwallon kafa na guragu da aka fi sani da Para Soccer da kungiyar da…

Duk da kasancewa ita taz o ta biyu a gasar wasan kwallon kafa na guragu da aka fi sani da Para Soccer da kungiyar da ke yaki da cutar foliyo ta shirya, shiyyar Kudu Maso Kudu, aka gudanar a garin Fatakwal na Jihar Ribas,kungiyar Kuros Riba United tana bukatar kulawa daga gwamnati da kuma masu hannu da shuni. .

Kyaftin din kungiyar Sale Ali Sani da akafi sani da SAS ne ya bayayna haka jim kadan bayan an kammala gasar Para Soocer a garin Fatakakwal.
Ya ce daga cikin kungiyoyi 12 da suka fafata a gasar, kungiyarsu ce ta zo ta biyu kuma ta lashe kofi daya daga cikin kofuna uku da ake sanya. Ya ce Jihar Kano ce ta zo ta farko yayin da mu kuma ’yan Kuros Riba muka zo na biyu yayin da Jihar Ribas ta zo ta uku inda aka ba mu kofuna saboda bajintar da muka nuna.
Sale Ali ya ce babban burinsu shi ne a samu yawaitar kungiyoyin nakasassu da yawa a fadin kasar nan da za su rika wakiltar jihohi da ma kasar nan a duk wata gasa da ta taso a ciki da wajen Najeriya.
Kyaftin Sale Ali ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shi ne rashin samun tallafi daga gwamnatin jiha da ta tarayya. Ya ce daga cikin kungiyoyi goma da wuya ka samu biyu da suke samun tallafi daga gwamnati kuma hakan na ci musu tuwo a kwarya. Ya ce saboda kishi ne ya sa suke taimakon junansu don gudanar da wasa.
A karshe ya yi kira ga Ministan harkokin wasanni da ya tallafa musu, don da alama bai san halin da suke ciki ba, inda ya ce yana da kyau Ministan ya rika halartar wasanninsu don ya gane wa idonsa irin basirar da Allah Ya ba su.