✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Global Right da Legal Aid Council za su taimaki shari’ar marasa karfi a Bauchi

kungiyar bayar da tallafi kan harkokin shari’a a Najeriya (Legal Aid Council in Nigeria -LACN),  za ta hada gwiwa da kungiyoyin al’umma da na kare…

Malam Isa Yuguda Gwamnan Jihar Bauchikungiyar bayar da tallafi kan harkokin shari’a a Najeriya (Legal Aid Council in Nigeria -LACN),  za ta hada gwiwa da kungiyoyin al’umma da na kare hakkin dan Adam, musamman Global Right, domin bin kadin shari’un mutanen da aka take musu hakki a kotuna da gidajen yari ko kuma dukkan wuraren da ake zaton ana tauye hakkin marasa galihu.
Lauya Shamsuddin Mohammed Toro na LACN ne ya bayyana haka a wajen wani taron bita da kungiyar Global Right ta shirya a Bauchi. Ta kira kungiyoyi ta horas da su game da yadda za su sanya ido wajen zakulo wadanda aka tauye musu hakki tsakanin al’umma domin gabatar musu saboda bin kadin wadanda ba su da hanyar daukar lauya ko kuma shiga cikin dawainiyar shari’a don a taimaka musu.
Barista Shamsuddin ya ce Legal Aid hukuma ce da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa don bin kadi da bayar da tallafin shari’a ga marasa galihu, don haka aikin Global Right na ilmantar da kungiyoyi kan wannan,  abu ne mai kyau, wanda zai taimaka a kare hakkin dan Adam, kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Ya ce a shirye hukumar take a duk lokacin da mutum ke bukatar tallafin shari’a ya zo ofishinsu a sakatariyar gwamnatin tarayya don bayyana kokensa don su bayar da wakilci tun daga matakin sasantawa har zuwa shari’a game da duk wani abu da ya shafi tauye hakkin dan Adam game da hakkin da ya kunshi sashe na hudu na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ba kowa hakkin yin walwala cikin rayuwarsa.
Ya ce wasu lokuta sukan kai ziyara gidan yari don wadanda aka tsare ba bisa ka’ida ba, su bi hakkinsu har a fitar da su. Akan samu mutanen da aka tsare tsawon lokaci babu wani laifi, ko kuma a kai mutum kotun da ba ta da hurumin sauraron karar, har sai an sauya zuwa kotun da ta dace. “A tuntube mu game da duk wani lamari na saba ka’ida, idan an gani a cikin al’umma”. Inji shi.
Sylbesta Yirbis na kungiyar kare hakkin yara ya yabi taron, kuma ya gargadi ’yan kungiyoyin kada su yi sanya wajen sanar da duk wata matsalar take hakkin dan Adam don bin kadin lamarin.
Jamila Idris danjuma daga kungiyar kare hakkin jama’a ta Kangere, ta ce an fadakar da su game da ba-daidai ake yi wa mata da yara, musamman a karkara, saboda haka za su tashi tsaye wajen fito abin da ake wa mutanen karkara don a bi musu kadi.
Shi kuwa danjuma Idris Jodi na kungiyar ci gaban Kangere cewa ya yi ya sami sabbin dabarun taimakawa wajen kare hakkokin mazauna karkara.