✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar direbobin tanka ta Jos ta yi sabbin shugabanni

A ranar Litinin ne kungiyar direbobin tanka ta kasa shiyyar Jos (PTD) ta zabi sabbin shugabanni. Sabbin shugabannin za su ja ragamar kungiyar zuwa shekara…

A ranar Litinin ne kungiyar direbobin tanka ta kasa shiyyar Jos (PTD) ta zabi sabbin shugabanni.

Sabbin shugabannin za su ja ragamar kungiyar zuwa shekara hudu.
Shugabannin da aka zaba sun hada da Alhaji danladi Muhammad a matsayin Shugaba da Alhaji Yawale Muhammad, Mataimakin Shugaba na I da Yakubu Abdullahi, Mataimakin Shugaba na II da Musa Muhammad, Ma’aji da dan’azumi Musa, Mai Binciken kudi.
Sauran shugabannin su ne Yusuf Senior, Sakataren Kudi da Alhaji Auwalu Muhammad , bIO da Mustafa Babansu, Jami’in Jin dadin jama’a da Hassan Halliru, Mai tsawatarwa da Alhaji Nabada, Mai bayar da shawara.
Sabon shugaban kungiyar Alhaji danlami Muhammad ya ce za su yi iya bakin kokarinsu wajen gudanar da mulki cikin adalci.
“Da yardar Allah za mu yi adalci a kan amanar da aka damka mana. Sannan ina kira ga ’yan kungiyar su ba mu goyan baya don tafiyar da shugabancin kungiyar cikin kwanciyar hankali.” Inji shi.