✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar daliban Najeriya ta yi addu’ar neman maslaha a Jihar Bauchi

kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta gudanar da taron addu’a na shiyyar Arewa maso Gabas a garin Bauchi, domin kai kokensu game da matsalar  yajin…

kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta gudanar da taron addu’a na shiyyar Arewa maso Gabas a garin Bauchi, domin kai kokensu game da matsalar  yajin aiki da suka fada tare da gama karatu ba aikin yi, lamarin da suka bayyana cewa yana kara sanya su cikin rudani da hadarin rayuwa.
Matamakin Sakataren kungiyar na kasa Kwamared Umar Adamu Jibrin, ya bayyana cewa dalilin shirya wannan taron addu’a da yin azumi a ranar arfa, shi ne mawuyacin halin da Najeriya ta shiga, amma sun fi bayar da karfi wajen Allah ya kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye harkar ilmi, yadda jami’o’i ke yajin aiki,  tare da manyan makarantu da suka fara.
Ya ce lamarin ya kai makura, shi yasa yanzu suka koma addu’a sun bar  zanga-zanga ko nuna bacin rai game da abin da ke faruwa.
Ya ce dalibai su na cikin wahala, malamai da mutanen gwamnati na walwala, inda ’ya’yan manya ke karatu a makarantun kasashen waje, illa su ’yan talakawa ke cikin wannan wahala, don haka yake gani lamarin ya zamo dole su koma ga Allah da addu’ar ranar tsaiwar arfa. Don haka sun yi hankali hawa titi don bore ya zama tsohon yayi gare su, musulmi da kirista duk sun shiga wannan aiki don neman maslaha.
Umar Adamu ya kara da yaba wa gwamna mai riko na Jihar Taraba, Alhaji Garba Umar wanda ya ba su kudin da suka shirya wannan taro, kuma sun gayyaci limamai da Pastoci kan wannan taro na shiyyar arewa maso gabas, sauran shiyyoyi suma suna gudanar da taron a duk Najeriya. Don haka su ma sun sanya shi cikin addu’ar fatar alheri da neman gamawa lafiya.
Kwamared Bashir Yakubu, shi ne shugaban kungiyar daliban Najeriya da kasashen waje na Jihar Taraba, cikin jawabinsa ya bayyana cewa sun dauki salon watsar da zanga-zanga don neman biyan bukata, saboda ko a cikin jami’o’i yanzu an fito da kwas na wanzar da zaman lafiya da daidaita sabani tsakanin al’umma.  Don haka su ma sun koma yin addu’a don gaya wa Allah damuwar su.