A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) ta bai wa Shugaban Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna Farfesa Aledander Kure lambar girmamawa na kasancewarsa shugaban kwaleji mafi fice, wanda ya yi zarra a cikin sa’o’insa na sauran kwalejojin kasar nan saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar da kuma kafa tarihi cikin kankanin lokacin da ya yi a makarantar.
Bikin karramawar, wanda aka gudanar da shi a ofishinsa da ke harabar makarantar da ke Gidan Waya a karamar hukumar Jama’a inda kuma uwar kungiyar ta kasa ta ba shi matsayin uban kungiyar nan take.
Yayin da ya ke jawabi, Daraktan Tafiye-tafiye na kungiyar, Kwamred Dominic Phillip ya jinjinawa shugaban bisa ga namijin kokarin da ya nuna musamman a wajen kwantar da hatsaniyar daliban makarantar a shekarar da ta gabata.
Shi ma da ya ke nasa jawabin, babban sakataren kungiyar, Kwamred Umar Farouk ya bayyana cewa wannan girmamawar ta hada har da duba irin gudummawar da shugaban ya bayar a fannin ilmi da rayuwa.
Yayin da ya ke maida jawabi, Farfesa Kure ya yabawa shugabancin kungiyar da ta ga dacewarsa da wannan girmamawar tare da jingina hakan bisa ga irin namijin kokarin da ya nuna wajen tafiyar da makarantar.